A ranar Alhamis, Gwamnatin Tarayya ta gano wani gunkin tarihi da aka sace daga Najeriya a birnin Mexico na kasar Mexico.
An damka gunkin tarihin a hannun Ministan Harkokin Kasashen Waje, Geoffrey Onyeama.
- An tallafa wa masu kananan sana’a’o’i da N100m a Konduga
- Matar aure mai sana’ar tuka Keke NAPEP a Kano
- Shin DSS ce ta azabtar da direban Buhari har ya mutu?
- Ana zargin Tambuwal da haddasa rikici a jam’iyyar PDP
Gunkin tarihin, ya samo asali ne daga garin Ife da ke Jihar Osun, a yankin Kudu-maso-Yammacin Najeriya.
Onyeama, ya ce an dawo da gunkin da aka sace aka sayar da sassansa ga kasashen duniya, gida Najeriya bayan ya shafe tsawon lokaci ana neman sa.
Ya kara da cewa tun a 2017, tsohon Jakadan Najeriya a kasar Mexico, Aminu Alhaji Iyawa, ya fara farautar gunkin a filin jirgin sama na Benito Juarez na kasar.
A cewarsa, bayan tsaurara bincike da Ma’aikatar Yada Labarai da Raya Al’adu ta Najeriya ta yi, an tabbatar da cewa gunkin na Najeriya ne tare da dawo da shi gida, don ci gaba da raya tarihi.