Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ce kayayyakin da Najeriya ta fitar zuwa kasar Amurka sun kai na Dala biliyan 1.9 a shekarar 2020.
Shugaba Buhari ya bayyana haka ne a lokacin da yake jaddada muhimmancin kara yawan kayayyakin da Najeriya ke fitarwa zuwa Amurka.
- Masu hannayen jari a Najeriya sun yi asarar biliyan N124 ranar Alhamis
- NAJERIYA A YAU: Halin da ’yan gudun hijirar Bama ke ciki bayan komawa garinsu
Hadimin shugaban kasa, Femi Adesina, ya ruwaito Buhari na cewa akasarin kayan da Najeriya ta fitar zuwa Amurka a 2020, albarkatun mai ne.
Ya kuma bayyana Amurka a matsayin babbar abokiyar hulda ta fuskar diflomasiyya da kasuwanci ga Najeriya.
Buhari ya bayyana haka ne a lokacin taron neman fahimta da bunkasa kasuwanci tsakanin kasashe, wanda Najeriya ta shirya a Amurka.
Gwamantin Najeriya ta shirya taron ne a daidai lokacin da ake gudanar da babban taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 77 a Amurkan.
Najeriya ta yi amfani da damar wajen tattaunawa da kuma zawarcin kasashe da kamfanoni masu zaman kansu domin zuba jari a kasarta.
“Ba arzikin mai da iskar gas kadai Najeriya ke da su ba, akwai wasu bangarori masu muhimmanci da kuma riba wadanda za ku amfana matuka idan kuka zo kuka zuba jari.
“Tatttalin arzikinmu shi ne mafi karfi a Afirka, ga mu da yawan ’yan kasa miliyan 200 da za su iya sayar wa hajojinnku iri-iri daga bangaren noma, kiwon lafiya, wutar lantarki, kimiyya da kere-kere, ababen amfanin yau da kullum da dai sauransu.
“Wani abu mai dadi game da wannan taro shi ne mun zo da ministocin da ke kula da duk wadannan bangarorin, da manyan ’yan kasuwarmu da za ku so yin hulda da su, ” in ji shi.