✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Najeriya na cin bashi don biyan albashi – Ngozi

Ministar Kudi Dokta Ngozi Okonjo-Iweala, ta ce Gwamnatin Tarayya na cin bashin kudi domin ta biya albashin ma’aikata saboda mummunan halin da tattalin arzikin kasar…

Ministar Kudi Dokta Ngozi Okonjo-Iweala, ta ce Gwamnatin Tarayya na cin bashin kudi domin ta biya albashin ma’aikata saboda mummunan halin da tattalin arzikin kasar nan ya fada ciki.

Kamar yadda ta bayyana, faduwar farashin man fetur a duniya ya sanya tun daga watan Janairun bana zuwa yanzu, gwamnati ta ci bashin fiye da naira biliyan 400.
Ministan ta ce: “Daga cikin naira biliyan 882 da aka amince a karbo bashi a cikin kasafin kudin bana, a yanzu haka gwamnati ta ci bashin naira biliyan 473 domin gudanar da ayyuka da kuma biyan albashi.”
Wannan labarin ba zai yi wa gwamnatin Janar Muhammadu Buhari wacce za ta karba mulki a ranar 29 ga watan nan ba, saboda kasancewa zai fara mulki ne a lokacin da tattalin arzikin kasar ke tangal-tangal.
Masu sharhi na ganin cewar matsalar tattalin arzikin na da nasaba da irin makudan kudin da aka kashe lokacin zaben da aka gudanar a kasar.
Kodayake, a shekaranjiya Laraba ministan ta musanta batun da ake yi cewa ma’aikatan Gwamnatin Tarayya suna bin bashin albashin watanni. Mai gana da yawunta Paul Nwabuikwu ya ce matsalolin da ake samu shi ne idan wasu gwamnoni sun kasa bin albashi, sai su daura laifin ga Gwamnatin Tarayya.