✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Najeriya Buhari yake so ba ’yan Najeriya ba – PDP

Ra’ayi ya bambanta a tsakanin magoya bayan Jam’iyyar APC da Jam’iyyar PDP a Jihar Bauchi game da sake tsayawa takarar da Shugaban kasa Muhammdu Buhari…

Ra’ayi ya bambanta a tsakanin magoya bayan Jam’iyyar APC da Jam’iyyar PDP a Jihar Bauchi game da sake tsayawa takarar da Shugaban kasa Muhammdu Buhari ya ce zai yi a badi.

Kakakin Jam’iyyar PDP Alhaji Yayanuwa Zainabari ya shaida wa Aminiya cewa su a Jam’iyyar PDP ba sa tsoron takarar Shugaba Buhari domin ya gaza cika alkawuran da ya dauka a lokacin yakin zabe.

Zainabari ya ce wahala da kuncin rayuwa da masifar tsadar kayayyaki sun sa talaka cikin halin kaico maimakon kyautata rayuwarsa da jam’iyya mai mulki ta yi alkawari.

Ya ce suna da ’yan takara nagari a PDP wadanda a cikinsu yanzu suna addu’a ne Allah Ya sa wanda zai fi zama alheri kuma ya yi kokari wajen warware matsalolin ’yan Najeriya ya zama dan takararsu. Zainabari ya ce a fahimtarsu Buhari Najeriya yake so amma ba ya son ’yan Najeriya tunda ya bar su a cikin kunci da wahala.

Sai dai Sakataren Kwamitin Labarai na Jam’iyyar APC na Jihar Bauchi Kwamred Aliyu Ilelah ya ce ba sa shakka cewa Buhari ne zai sake lashe zabe a 2019 domin a cewarsa har yanzu ’yan Najeriya ba su ga dan takarar da ya kai Buhari dattako da kishin kasa da kuma gaskiya da adalci ba.

Aliyu Ilelah ya ce a Bauchi tun kafin Buhari ya ce zai tsaya takara ma wadansu suka yi ta zanga-zanga suna kiransa ya fito takara saboda gamsuwa da ’yan Najeriya suka yi da mulkinsa da kokarinsa ta fuskar tsaro da gina tattalin arziki mai dorewa.