Gwamnatin Tarayya ta ce Najeriya ba za ta taba rushewa ba duk da irin kalubalen da kasar ke fuskanta.
Hakan ya fito ne daga bakin Ministan Yada Labarai da Raya Al’adu, Lai Mohammed a wajen wani taro ranar Litinin a Legas.
- ’Yan sanda sun watsa casun tsiraici a Adamawa
- Me ya sa El-Rufai bai yi ta’aziyyar Iyan Zazzau ba?
- Gwamnatin Buhari ce ta lalata Najeriya —PRP
- Shirme ne kiran Buhari ya yi murabus —Gwamnatin Tarayya
“Wannan ba zai taba faruwa ba, Gwamnatin Najeriya na samun galaba a kan ayyukan ta’addanci da garkuwa da mutane,” inji shi.
A baya Aminiya ta rawaito cewa, jaridar ‘Financial Times’ ta birnin London, ta ce Najeriya na iya rushewa saboda matsalolin da suka addabi kasar.
Sai dai Lai Mohammed ya soki jarida, inda ya ce hakan ba za ta taba faruwa ba domin Najeriya ke samun nasara a yaki da ta’addanci da garkuwa da mutane.
Ya kara da cewa duk masu yi wa kasar fatan rushewa ba za su taba ganin wannan rana ba.
A cewarsa, a shekarun 2010 da 2011 yayin bikin Kirsimeti bom ya kashe mutane da yawa.
Amma a wannan karon babu ire-iren wadannan tashe-tashen hankulan, kuma Gwamantin na kokari wajen ganin bayan ayyukan ta’addanci.
Ministan ya bayyana shekarar 2020 a matsayin shekara mai cike kalubale, inda aka yi fama da cutar COVID-19, zanga-zangar #EndSARS da kuma matsalar tsaro.
Sai dai ya ba da tabbacin cewa a 2021 kasar za ta samu cigaba, sannan za ta fita daga karyewar tattalin arziki da ta samu.