✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

NAJERIYA A YAU: Yadda ’Yan Ci-rani Ke Safarar Makamai Zuwa Arewa

Shi me ya sa ’yan Arewa shiga harkar fasakwaurin makamai alhali da makaman ’yan bindiga ke kashe al’ummomin yankinsu?

More Podcasts

Domin sauke shirin kai tsaye, latsa nan

A lokacin da ake faman yaki da ta’addanci a Najeriya, an kama wadansu ’yan ci-rani dauke da buhunan albarusai da miyagun kwayoyi a wata tashar mota a Jihar Legas a karshen makon da ya gabata.

Wadanda ake zargin ’yan Arewa ne kuma suna hanyarsu ne kai makaman zuwa yankunansu; Shi me ya sa suka fada wannan muguwar sana’a?

Saurari shirin Najeriya A Yau domin sanin yadda abin ya faru da wadanda aka kama.