More Podcasts
Bayanai na ƙara bayyana game da wani hari da Rundunar Sojin Sama ta Najeriya ta kai a kan wasu ƙauyuka biyu na Ƙaramar Hukumar Maradun ta Jihar Zamfara, wanda ya yi sanadin mutuwar fararen hula aƙalla 15.
Waɗanda suka shaida faruwar lamarin dai sun ce sojojin sun kai hari da jirgi mai saukar ungulu ne a ƙauyukan biyu waɗanda ’yan bindiga suka kaiwa hari .
Wannan na zuwa ne makonni kusan uku bayan da Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya ta kai wani harin irin wannan a Ƙaramar Hukumar Silame da ke Jihar Sakkwato wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama.
- NAJERIYA A YAU: Abin Da Ya Sa ’Yan Najeriya Ba Sa Samun Wadataccen Abinci
- DAGA LARABA: Yadda sunayen zamani suka shafe na Hausawa
Shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci zai yi duba ne kan abin da ya biyo bayan harin.
Domin sauke shirin, latsa nan