Wasu da ake zargin mayaƙan Boko Haram ne sun kai hari kauyen Izge da ke Ƙaramar Hukumar Gwoza a Jihar Borno, inda suka kashe sojoji tare da rasa mayaƙansu da dama.
Rahotanni na cewa harin ya auke ne da misalin karfe 1:00 na ranar Lahadi a lokacin da ’yan ta’addan suka mamaye sansanin sojin Nijeriya da ke garin Izge.
- Zanga-zangar da za mu yi babu gudu babu ja da baya — Take It Back
- An sayar da kare mafi tsada a duniya
Wata majiyar tsaro ta tabbatar wa Aminiya cewar wani soji mai muƙamin Kyaftin da kuma Kofur na daga cikin waɗanda suka kwanta dama, yayin da sojoji suka yi nasarar hallaka mahara da dama a yayin arangamar.
Shugaban ƙaramar Hukumar Gwoza, Hon. Abba Kawu Idrissa Timta, ya tabbatar da faruwar lamarin.
Sai dai ya ce har yanzu lokacin da aka tuntuɓe shi ba a kai ga tantance irin asarar da rayuka daga ɓangarorin biyu ba.
“Sai dai muna tabbatar da kashe ’yan ta’adda da dama,” a cewarsa.
Bayanai sun ce mahara da dama haye a kan babura sun mamaye sansanin sojojin, bayan da suka harba makamin roka da ake kira RPG a kansu.
Rahotanni sun ce, da farko sun kama hanyar nasara a kan sojoji, sai daga bisani mafarauta da ’yan banga suka ƙara ƙwarin guiwa har ta kai ga fatattakar maharan.
Majiyoyi sun ce sojoji da mafarauta da jajirtattun mazauna garin ne suka fatattaki ’yan ta’addan da ke tserewa zuwa dajin Sambisa.