More Podcasts
A daidai lokacin da ake tunanin samun sauƙi daga tarin matsalolin tsaro da na tada ƙayar baya a Najeriya, sai ga wasu sabbin matsalolin na ƙara kunno kai.
Yayin da a wannan lokaci ake fuskantar hare-haren da ake zargin na ƙungiyar Boko Haram ne a Arewa maso Gabas, da kuma sabbin kashe-kashe a sassan jihohin Filato da Binuwai, sai kuma ga wata sabuwar ƙungiya da ake zargin ta ’yan ta’adda ce mai suna Mahmuda ta ɓulla a Jihar Kwara.
To ko mene ne ya haddasa wannan koma-baya ta fuskar tsaro?
Shin a ganinku, me ya sa matsalar tsaro “ta gagari gwamnatin” Najeriya?
- NAJERIYA A YAU: Sabbin dabarun hana matasa aikata laifi
- DAGA LARABA: Dalilan Ɓaraka A Tsakanin Iyayen Riƙo Da Ƴaƴan Riƙo
Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan dalilan ƙara ƙazancewar matsalar tsaro da hanyoyin magance su a Najeriya.
Domin sauke shirin, latsa nan