More Podcasts
Kudurorin Dokar Haraji da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya aike wa Majalisar Dokoki ta Ƙasa suna ci gaba da tayar da kura a Najeriya.
Muhawara a kan batun ta dauki sabon salo ne bayan da wasu malaman addinin Musulunci daga Arewacin Najeriya suka ki amincewa da wasu tanade-tanaden ƙudurorin dokar.
- NAJERIYA A YAU: Dalilin ƙulla yarjejeniyar Gwamnatin Kaduna da ’yan ta’adda
- DAGA LARABA: Abin ya sa ’yan Nijeriya ke kishin ƙabila fiye da ƙasa
Shin har da su kaza ne a cin danko? Karambani ne ya sa malamai tsoma baki a muhawarar ko neman maslaha ga al’umma? A kan waɗannan batutuwa shirin Najeriya A Yau zai yi nazari.
Domin sauke shirin, latsa nan