More Podcasts
Ɓarnata kayan gwamnati ba sabon abu ba ne a Najeriya; sai dai a wannan karon barnar ba gwamnati kadai ta shafa ba, har ma da al’ummar gari.
A kwanakin baya ne wasu yankuna na Arewacin Najeriya suka fuskanci rashin wutar lantarki na tsawon kusan kwanaki goma.
A cewar hukumomin da abin ya shafa dai, hakan ya faru ne saboda ’yan ta’adda sun kai wa turakun wutar lantarki hari.
- NAJERIYA A YAU: Dalilan Durƙushewar Ƙananan Sana’o’i Da Hanyoyin Magance Su
- DAGA LARABA: Tarihin Almajirci a kasar Hausa da yadda yake a da
Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi duba ne a kan abin da ya hana kawo ƙarshen ɓarnar da ake yi wa layukan dakon wutar lantarki.
Domin sauke shirin, latsa nan