Hukumar kula da Aikin Hajji ta Nijeriya (NAHCON), ta fitar da sharuda da ka’idojin da maniyyata Umrah za su cika kafin su samu amincewar tafiya aikin ibadar a Kasa Mai Tsarki.
Dokokin da NAHCON ta fitar ta shafinta na Facebook su ne kamar haka:
- Matafiyi ya kasance daga shekara 18 zuwa 50
- An yi artabu tsakanin jami’an tsaro da masu zanga-zangar Iraki
- #EndSARS: Farashin shinkafa ’yar waje ya fadi warwas
- Nuna takardar shaida daga amintaccen wurin gwaji cewa ba ya dauke da cutar coronavirus.
- Kar wuce sa’a 72 daga lokacin gwajin kafin tashi daga filin jirgin sama zuwa kasar Saudiyya.
- Kiyaye ka’idojin neman izinin ziyara zuwa Masallacin Annabi (S.A.W) da zuwa addu’a Rawdha kamar yadda aka gindaya.
- Shaidar amincewar ranar tafiya da dawowa.
- Killace kai na tsawon kwana uku a masauki kafin fara gabatar da aikin Umrah.
- Samun abun hawan zirga-zirga daga filin jirgi zuwa masauki.
- Samun abun hawa domin zirga-zirga daga masauki zuwa Harami da Mikati.