Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Najeriya (NAFDAC) ta rufe masana’antun madarar yogot guda hudu a Kaduna.
Shugaban Ofishin NAFDAC na Jihar Kaduna, Nasiru Mato, ya sanar da manema labarai a ranar Juma’a, 8 ga watan Oktoba, 2021 cewan an rufe kamfanonin ne saboda ba su da lasisi.
- Matsalar tsaro: Gwamnonin Arewa za su yi taro da na Nijar
- Yadda Buhari ya gabatar da kasafin 2022 na N16.39tn
Ya ce: “Ruwa da dukkannin abubuwan da ake sarrafawa da madara suna da matukar muhimmanci a ba su kulawa ta musamman don kare al’umma daga cin gurbatattun abubuwa”.
An gano kamfanonin madarar ne a lokacin da jami’an NAFDAC suke zagayen duba tsafta da ingancin abubuwan da kamfanoni ke sarrafawa, don tabbatar kare lafiyar masu amfani da su.
Nasiru Mato ya kara da cewa wannan ne ya sa NAFDAC ke kara sanar da al’umma cewa ya zama wajibi ga duk masu sarrafa irin wadannan abubuwa da su tabbatar sun bi kai’dojin da hukumar ta sa don kauce wa matsalar da za ta iya haifarwa.
Daga karshe ya ce za su cigaba da bincike a dukkanin lungu da sakon jihar.