Wasu ’yan bindiga sun nemi a ba su Naira miliyan 100 kafin su sako wani fasto da suka yi garkuwa da shi a Jihar Kaduna.
Faston, mai suna Samson Ndah Ali, mai shekaru 30, yana aiki da cocin Evangelical Church Winning All (ECWA) da ke Mararaba Aboro, a Ƙaramar Hukumar Sanga.
- Mutanen da suka saba ba ni abinci yanzu na neman taimako — Obi
- ’Yan bindiga sun mamaye garuruwa 64 a Filato — Gwamna Mutfwang
An sace shi da misalin ƙarfe 1 na daren ranar Litinin, lokacin da ‘yan bindigar suka shiga gidansa.
Faston ya fara aiki a cocin ne ƙasa da makonni biyu kafin wannan lamarin ya faru.
Sakataren cocin, Yusuf Ambi, ya ce yana tare da Faston a daren da lamarin ya faru.
Ya ce washegari an kira shi a waya aka sanar da shi cewa faston ya ɓace.
Da ya isa gidansa, ya tarar ƙofofin a buɗe babu kowa a ciki.
Daga bisani, maharan suka kira, suka nemi a ba su Naira miliyan 100 a matsayin kuɗin fansa.
Ambi ya ce har yanzu suna tattaunawa da maharan.
Dakarun tsaro da suka haɗa da sojoji, ’yan sanda da jami’an DSS sun fara aiki tare don ceto faston.
Kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Kaduna, DSP Mansir Hassan, ya ce zai yi bayani daga bisani.