Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Kasa (NAFDAC), ta gargadi ’yan Najeriya da su guji amfani da wasu magungunan tari da ke kasuwa yanzu haka.
NAFDAC ta bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na Facebook a ranar Litinin.
- Kwana 3 bayan kashe Limamin coci, matasa sun kone ofishin ’yan sanda a Neja
- Muna da hujjoji kan cewa Tinubu tsohon mai laifi ne – Dino Melaye
A cewar hukumar, “NAFDAC na sanar da jama’a cewa, akwai wasu magunguna biyu da ba su da inganci wadanda suka hada da Ambronol da DOK-1Max da aka gano a kasar Uzbekistan da Nahiyar Turai, wadanda Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta sanar.
“Gwaje-gwajen da ma’aikatar lafiya ta Uzbekistan ta yi, sun nuna cewa, magungunan na dauke da wasu nau’ukan sinadarai na diethlene glycol/ethylene glycos da suka kasance gurbatattu,” a cewar NAFDAC.
Hakan ya sa hukumar ta nemi al’umar Najeriya da su guje wa yin amfani da wadannan magungunan.
“Idan kuna da wadannan magunguna, kada ku yi amfani da su. Idan kai, ko wani da ka sani ya yi amfani da wadannan magunguna, ko kun fuskanci wata matsala bayan amfani da su, ana ba ka shawara da ka garzaya asibiti don a duba lafiyarka.”