Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Kasa (NAFDAC) ta dakatar da kamfanin Mars Remedies PVT Limited na kasar Indiya shigo da magungunansa Najeriya bisa zargin yin na jabun.
Shugaban NAFDAC, Farfesa Mojisola Christianah Adeyeye, ta ce an dakatar da kamfanin ne saboda yin jabu kwayar maganin Ciprofloxacin BP 500mg mai lamba NAFDAC REG. NO C4-0498.
- NAFDAC ta garkame kamfanonin kera magungunan jabu a Kano
- NAFDAC ta kwace magungunan Naira biliyan 3 a shekara
- An sace magunguna masu hadari a ma’adanar NAFDAC
Mojisola ta ce, Mars Remedies ne ke yi wa Pinnacle Health Pharmaceutical Ltd, na Najeriya da ke Legas magunguna.
Ya ce matakin da aka dauka zai magance sake aukuwar hakan sannan ba za a bari duk wani maganin da kamfanin ke yi ya shigo Najeriya ba.
Daga karshe ya bukaci kamfanonin magani na cikin gida da masu shigowa da suka bi ka’idojin da aka yi musu rijista don kauce wa dakatarwa.