✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Na yi wa mata 50 fyade da fashi a gidaje 100

'Abin da ya sa ni shiga harkar fashi bayan rabuwa da budurwata'

An cafke wani hatsabibin matashi bayan ya yi wa kimannin mata 50 fayde da aikata fashi a gidaje daban-daban.

Da yake amsa tambayoyi, wanda ake zargin ya ce ya yi amfani da tsibbu wurin yi wa mata sama da 50 fyade da kuma fashi a gidaje sama da 100.

“Duk lokacin da ake yin wani biki sai shiga in na nuna kamar ina daga cikin wadanda suka shirya taron.

“Ina da wani mabudin abin sha na musamman da nake amfani da shi in bude wa masu hannu da shuni ababen shansu, ta hakan nake samun wadanda ke fadawa a tarkona.

“Na yi wa mata kusan 50 fyade; Duk lokacin da zan yi wa mace fyade zan tabbatar cewa na yi aiki da dare kuma matar za ta fada tarkona bayan amfani da layuna.

“Zan kuma tabbatar na rufe fuskarta yayin da nake cikin aikin.

“Na dade ina wannan aika-aikar tunda na rasa komai kuma mai gidan da naha yaha ya tashe ni daga gidansa.”

Ya bayyana cewa ya shiga mummunar sana’ar ce bayan al’amura sun dagule masa har ta kai ga budurwar da zai aura ta juya masa baya ana dab da daurin aurensu.

“Ina da wata budurwa da ta bar ni ta koma wurin wani mutum lokacin aurenmu da ita ya kusa.

“Na yi bakin ciki da takaici shi ya sa na tsunduma cikin harkar fashi  wanda nake gani ya fi min riba,” inji shi.

Jami’an tsaron yankin Yarbawa ma Amotekun ne suka cafke hatsabibin mai shekara 46, bisa zargin sata a Owo, hedikwatar Karamar Hukumar Owo ta Jihar Ondo.

Kwamandan Amotekun na Jihar Ondo, Cif Adetunji Adeleye, ya bayyana cewa an yi nasarar kama wadanda ake zargin ne a yayin wani aikin sintiri.