Wani magidanci da ya kware a harkar dinkin sirfani a Jihar Legas, mai suna Umar Alin Gabari ya ce ya zabi yin sana’ar sirfani saboda ta fi kasuwanci a wurinsa.
Umar Alin Gabari, mai shekaru 41, dan asalin Jihar Kano ya yi furucin haka ne yayin da yake tattaunawa da Aminiya a shagonsa da ke Legas a karshen makon da ya gabata.
Ya ce, “Ba na sha’awar wata sana’a kuma ba na sha’awar wani kasuwanci. Sana’ata ta sirfani ta fi mini dukkan sauran sana’o’i, saboda babu abin da na rasa a cikinta. Na yi gida, na yi aure, kuma ina samun abin da nakan biya bukatuna na yau da gobe. Musamman kuma ina taimaka wa iyayena da ’yan uwana, a cikin wannan sana’a ta sirfani da na yi shekaru 23 ina gudanar da ita, saboda haka na gode wa Allah Madaukakin sarki”.
Ya ci gaba da cewa, “Na yi karatun boko tun daga firamare har zuwa sakandare. Wani kanen mahaifinmu ne ya sanya ni a cikin harkar dinkin sirfani kuma tun lokacin da na fara zuwa yanzu, sai cigaba nake samu da nasarori da yawa a kullum”.
Umar, wanda ya ce kodayake koyon aikin sirfani yana da cin rai, amma duk da haka ya bayyana cewa yana mutukar sha’awar sana’ar.
Daga nan sai ya ce hakuri da juriya ne suka sanya shi ya cimma burin da ya sa a gaba.
Ya yi watsi da zargin da wasu ke yi wa masu sana’ar dinki na saba alkawari, inda ya ce, “Gaskiya ba haka ba ne. Ba duk masu harkar dinki ne ke saba alkawari ba. Ni gaskiya, ina mutukar kokarina na kiyaye alkawari. Idan na sanya maka lokaci, to babu shakka, cikin yardar Allah, zan yi dukkan iya kokarina na ga na cika maka alkawarin, idan ka zo karbar aikinka za ka samu ba tare da wata matsala ba. Ina godiya ga Allah da Ya taimake ni a kan haka”.
Ya yi kira ga masu sana’a irin tasa, su rika cika alkawari don yin haka ne zai sa jama’a su amince musu.
Na yi gida, na yi aure a sana’ar dinkin sirfani – Umar Mai Sirfani
Wani magidanci da ya kware a harkar dinkin sirfani a Jihar Legas, mai suna Umar Alin Gabari ya ce ya zabi yin sana’ar sirfani saboda…