✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari ya rasu a wani asibiti a Landan

Buhari ya rasu ne a ranar Lahadi a Birnin Landan, bayan fama da rashin lafiya.

Allah Ya yi wa Tsohon Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari, rasuwa a yau Lahadi.

Wannan na cikin wata sanarwa da mai magana da yawun tsohon shugaban Garba Shehu, ya wallafa a shafin X (twitter).

Buhari ya rasu ne bayan ya sha fama da rashin lafiya.

Sanarwar ta ce: “Inna Lillahi wa Inna ilaihi raji’un. Iyalan tsohon shugaban ƙasa, suna sanar da rasuwar Tsohon Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari da rana yau a wani asibiti da ke birnin London.

“Allah Ya jiƙansa, Ya gafarta masa, ya sa Aljannatul Firdaus ce makomarsa. Amin,” in ji sanarwar.

A makon da ya gabata ne Garba Shehu, ya sanar da cewa Buhari na fara da matsananciyar rashin lafiya, amma ya fara samun sauƙi.

Buhari ya rasu yana da shekaru 83 a duniya, ya bar mata ɗaya da ’ya’ya da kuma jikoki.

Batun rashin lafiyar na tsohon shugaban ƙasa ya haifar da cece-ku-ce, inda tsohon hadimin Buhari, Bashir Ahmad, ya ce rashin lafiyar ba matsananciya ba ce.

Tuni dai al’umma suka fara nuna alhininsu game da tsohon shugaban na Najeriya.

Buhari, ya mulki Najeriya sau biyu a tarihi, ya mulkr ta a lokacin mulkin soja, sannan ya sake mulkarta a lokacin mulkin dimokuraɗiyya.

Ya mulki Najeriya daga 2015 zuwa shekarar 2023, inda Shugaba Tinubu ya gaje shi a ƙarƙashin jam’iyyar APC.