✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Na shirya wa sammacin Atiku —Tinubu

Jam'iyyar APC ta ce kamata ya yi Atiku ya gode wa Allah da bai kare a mataki na uku ko na hudu a zaben ba.

Sabon zababben shugaban kasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya ce ya shirya tsaf domin tunkarar duk wani sammaci daga dan takarar Jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, zai yi masa.

A wani taron manema labarai a ranar Alhamis, Atiku ya ce zaben na ranar Asabar da ta gabata wanda Hukumar Zabe ta Kasa (INEC), ta sanar cewa Tinubu ya lashe, a matsayin zabe mara inganci.

Sai dai a wani martani da ya mayar da Festus Keyamo (SAN) ya fitar, Tinubu ya ce, “Shirin Atiku Abubakar na kalubalantar sakamakon zaben abin farin ciki ne.

“Mun shirya don tunkarar kalubalensa, kowane iri a ko’ina sannan a koyaushe.

“Idan Atiku Abubakar ba zai iya goya wa zababben shugaban kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu baya ba, abin da ya fi masa shi ne sali-alin ya koma Dubai da zama.

“Atiku Abubakar ya yi murna bai zo na uku ko na hudu a zaben ba, saboda da sai ya fi fuskantar tozarci.

“Na farko, Atiku Abubakar ya karya ka’idar shiyya-shiyya a cikin jam’iyyarsa ta hanyar dagewa sai ya tsaya takarar shugaban kasa.

“Bayan fitowa takara, ita kanta PDP ta ci gaba da yi wa shugabannin Kudancin jam’iyyar zagon kasa, ta hanyar bai wa Atiku takara.

“Wannan ba shakka ya haifar da tawaye daga gwamnonin G-5 tare da yi wa PDP zagon kasa kafin zabe da kuma a rumfunan zabe.

“Rashin hada kan jam’iyyarsa shi ne dalilin da ya sa ya fadi zabe,” in ji Festus Keyamo.

Atiku dai kamar abokin hamayyarsa na jam’iyyar LP, Peter Obi ya ce ya shirya zuwa kotu don kalubalantar nasara Tinubu a zaben na ranar 25 ga watan Fabrairu.