Lawallin Bela shahararren dan dambe ne da ya tari aradu da ka inda ya shiga dambe don ya dauki fansan kisan abokinsa da aka yi. Ya kuma fada wa Aminiya sirrin ’yan dambe na da, da na yanzu.
Mene tarihin ka?
Suanan Lawallin Bela, Shekaru na 70. An haifeni a garin Bela, da k karamar Hukumar Bungudu ta Jihar Sakkwato. Watau an haifeni ne a zamanin Sarkin Musulmi Abubakar na Uku. Kuma da ni aka yi siyasar Sardauna.
Ya akayi ka fara wasan dambe, ko ka gada ne?
Gadon gidan mu kira, kuma ban manta ba. Ina kuma noma har yanzu a nan birnin Kaduna. Amma Sana’a ta a yanzu shi ne kwangilar sare itatutuwa in aikin na da yawa, sai in sa masu inji su taya ni. Dalilin fara dambe na shi ne, ina da aboki da ake kira Ibrahim -Iro- Dogo wanda a yanzu ina auren ’yarsa. Shi mutumin kauyen Nahuce ne. Da suka raba rana a wurin dambe, sai Kanti dan kauyen Gusau ya buge shi, abin ya bata min rai, hankalina ya tashi. Sai nace sai na daukar wa abokina fansa. Suka kkra haddwa a Tudun Wada Gusau, ya kara kashe abokina.
Na fara dambe ina da shekara ashirin da ’yan kai a garin Kwantagora, kuma na yi shekaru goma sha uku ina dambe. Na fara ne da wani mai suna Dandi a lokacin ana garabasar kudi ta Udoji, watau a lokacin mulkin Janar Yakubu Gowon. Ana yi min dariyar cewa ga sabon dan dambe, am samu garabasa, don an ga dogon da ba a sani ba, ana min kallon haka-haka. Muka yi dambe, shi ma dogo ne kamar ni a kofar fadar Sarkin Kwantagora. Na same shi a hanci na naushe shi, jini ya yi ta zuba. Bai fadi ba amma aka raba. Sarkin Sudan ya jefo Naira goma guda hudu, shi biyu ni biyu. Da gari ya waye sai dangara Bahago ya tare ni dambe shi ma na yi masa kwaf daya, ya fadi kasa warwas, ko rama bugu bai yi ba.
To a lokacin a wane bangare kake?
Ina bangaren Arewa ne watau bangaren su Shago. Amma a Arewan muna “Jamus” ne. Jamus shi ne in kuna bangare daya da wani, amma yana yi maka kallon banza, sai ka ce ku debe raini. Da tashe na na bullo. An kashe Janar Murtala ina garin Yawuri ina wurin Sarkin noma Tanimu. Sai na nufi Fandogari. Muka raba da dahiru na buge shi. Ashe Ado dan-Kwaure da Bagobiri-Mai-Kayan-Fada suna wurin, ni ban sani ba.
Wane babban dan Dambe ka fara buge wa?
Bagobiri na fara bugewa lokacin Shinge ne makadinsa, ni kuma Kambo dan Gusau ne makadi na. Na yi masa kwaf daya. Fili ya yamutse, karuwai na kuka, samari na neman su buge ni don suna son shi, ni kuma dattijai ke so na. Sai wani mai kudi Alhaji Mamman Dogo ya je gida ya dauko yadin shadda “Targan” mai zane ya ce a sa mani, ya kuma gayyato ‘yan sanda ya ce su kare lafiyata.
Sai aka dauko Dodo dan Hadeja don ya kashe ni. Shi kuma Alhaji Mamman Dogo ya ce na gama damben Fandogari. Na ce ya barni in kashe, amma ya hana, ya biya min kudin mota zuwa Kaduna Kingsway amma ba a dambe, sai na wuce Funtuwa inda Mamman Shata ya sa min fam biyar a matsayin kazan karfi, sai wani bahago mai suna Ashana ya dauki kudin, na yi masa kwaf daya, ko rama bugu bai yi ba ya fadi. Na karbi fam biyar din. dan Dambe a lokacin mu bai damu da kudi ba, sai dai neman suna, ya ba makada da Maroka da Malamai da kuma yaran da ke bin mutum.
Wa ke ba ku masauki da daukar nauyin ku?
kungiyar dambe ke daukar nauyin mu. Suna samun kudin ne daga kudin shiga kallo watau (ticket). Na je Gusau, ana cewa baa sanni ba, na kashe Kanti Gusau, da Sule Mai-Jikin-Mata, da ‘Yar-Hudu, Dodo Ddn Hadejia da kuma Maikudi. Bayan nan muka buga da Ado dan Kwaure, ya kashe duk a Gusau. Sai dambe ya koma Sakkwato. Manya irinsu Shago na wurin. Duk inda na yi dambe Shago na wurin sai dai guda daya watau na Fandogari.
Mene ne abin ban mamakin day a faru da kai a dambe?
Ni da Ado dan-Kwaure mutumin Gumel ne, sannan shi kuma Kwaure wani Malami ne a garin Saminaka. Ban san ko ya yi karatu ne a wurinsa ba. Ado dan Kwaure shi ya fara kashe ni a Gusau. Muka taho kofar Mata Kano ya kashe ni, muka taho Jos, na kashe shi. Muka tafo Kafanchan na Kashe shi. A Kano Kings-Garden na kashe shi. A Damagaram na Kashe shi daga nan bai kara yin dambe ba . Ya kashe ni sau biyu, na kashe shi sau hudu. Sannan a Jos na buge Dogon-Daki-Daka, da zai fadi sai wani Mai-Rabo-Da-Gora ya rugo zai yi ceto, da na ga sa’a ta zo amma za a bata, sai na fara buge Mai-Gora sannan na buge Dogon-Daki-Daka.
Ka yi damben Target?
Na yi lokacin Na-Hantsi-Tureta yana Arewa. Shi ya kashe Ado-dan-Kwaure a Damben Taget. Sai dan-Anache ya yi mai zanbo. Duk wanda ya kashe gwanin dan Anache to sai ya yi masa Zambo. Ya yi ma Na-Hantsi-Tureta zambo yana cewa (…Badakkare koma Zuru tunda karnai sun kare…)
Wane Zambo dan-Anache ya yi maka, kuma mene dalili?
Yana cewa ne (…mun kashe kwazo, mun kashe Dandi, mun kashe kwatta balle Lawalli marigayi…). Dalilin yin zambon shine,
Dalilin da ya sa nayi bakin jini wurin dan Anache shi ne duk wanda zai yi wa kida na buge su. Da zan buge Gundumi a Sokoto dan Anache ya rugo ya rike sh. Amma bai ji da dadi ba, don ’yan kallo sun zuba masa kasa. Don ya bata wasa. Kuma duk Sakkwato babu wanda ya buwayi Umaru Gundumi-Na-Karime wurin dambe in ba ni ba. Na yi mai kisan dafe, watau ka bugi abokin karawa, amma hannunsa ne kadai ya taba kasa, ba jikinsa ba. Shi ma ya kashe ni. Amma ya fi jin zafin damben Maradi da mu kayi. Don ana son shi a Maradi sosai. A can ma dafawa ya yi sai aka tashi damben muka dawo Katsina. A dambe akwai kisan tsaye, mutum ya sume. Kuwa na faduwa a dambe, ko dan waye. In wani bai kashe ka ba, wani zai kashe ka.
Amma an ce Shago da dan Dunawa ba su taba faduwa ba?
Muna da tarihin dan-Dunawa, an ce an taba kashe shi a kasarsu, amma kowa ya ce maka ya ga faduwar Shago, ya fadi karya, don shi Sadauki ne a Dambe.
Akwai wanda ka taba kashewa ya mutu warwas?
A’a. Sai dai mutum ya suma. Amma a damben Yawuri, Yahaya Bazamfare ya buge yaron Gulmawa ya mutu, Shago ya ce a ci gaba da dambe. Kuma akwai wadanda suka mutu a gabana. Sannan a Kaduna a damben dan-China da Sani Gulmada, dan-China ya harbi Sani da kafa a zuciya ya yi luu zai fadi sai zaren Sani ya ware, ya dauko ya daura sai ya mike tsaye sai ya ciji yatsunsa. Ya fadi da baya keyarsa ta bugi kasa, aka dauke shi a mota amma daidai gidan yarin Kaduna ya mutu. Da muka je asibiti, sai Likita ya ce “sori” ya mutu. Mun yi masa jana’iza a Unguwar Rimi.
Me ya sa ka bar dambe?
Ilmin addini ya wadata, kuma na ji wa’azi ya ratsa ni. kuruciya ta sa ni dambe, don lokacin akwai jahilci. Yanzu mun tuba, mun bar dambe. Kuma gara in yi dambe da in yi tauri.
Ko za ka yi mana kirarin ka?
A’a. Na tuba na bar wannan harkar ta bala’i.
Wane shawara za ka ba ’yan Dambe?
Dambe ya mutu, don ‘Yan dambe sun kashe dambe. Don lalacewa, abokin dan Dambe sai ya rungume abokin shi in zai fadi, wai ceto ne don kar ya fadi. A lokacin mu, in ka taho ceto, kasa ka yi. Ba zan barka ba. Kuma yin wasan dare bai dace ba. Ba zan bar kanne ko ‘ya’yana su yi dambe ba.
Ko yaran Shago, dandunawa da Kai-Kadai-Gayya sun yi dambe?
Dan Kai-Kadai-Gayya mai suna Mamman habbe ya yi dambe amma ya yi saurin bari. Ba ka zama gwani, ka haifi gwani.