✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama matashi da kawunan mutane a Legas

Ana zargin cewa matashin yana kai kawunan Jihar Edo wajen wani boka — wanda yake amfani da su don yin kuɗi.

Rundunar ’yan sandan Jihar Legas ta cafke wani mutum mai suna Samson Oghenebreme a unguwar Odomola ɗauke da kawunan mutane.

Sanarwar da kakakin ’yan sandan Legas, Benjamin Hundeyin ya fitar, ta ce an kai kawunan da aka gano asibiti a Epe, yayin da ake ci gaba da bincike kan lamarin.

An kama matashin ne ɗan shekara 25 bayan da jami’an bijilanti da ke sintiri a yankin suka sanar da jami’an tsaro cewa ba su yadda da take-takensa ba.

Gidan Talabijin na Channels ya ruwaito cewa ’yan sandan sun yi zargin cewa matashin yana kai kawunan Jihar Edo wajen wani boka — wanda yake amfani da su don yin kuɗi.

Kwamishinan ’yan sandan jihar, CP Olohundare Jimoh ya yaba wa jami’an ’yan sanda da na bijilanti kan ɗaukar matakin da ya dace da sauri.

Ya kuma buƙaci duk mazauna jihar da su riƙa sa ido da kai rahoton abin da ba su yarda da shi ba zuwa ga ofishin ’yan sanda mafi kusa.