✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Na sanya kofi ne don hana matasa shaye-shaye -Malam Niga

Malam Yusuf Maduro da aka fi sani da Malam Niga, fitaccen mutum ne da ke kula da cibiyar da ya kirkiro mai kula da masu…

Malam Yusuf Maduro da aka fi sani da Malam Niga, fitaccen mutum ne da ke kula da cibiyar da ya kirkiro mai kula da masu tabin hankali ko kangararrun matasa da ke shaye-shaye.  A wannan karo ya sanya kofi ne inda kungiyoyin kwallon kafa 16 suka fafata a yankin Rigasa.  Aminiya ta samu zantawa da shi inda ya yi mata bayanin yadda gasar ta kasance kamar haka:

Zan so ka gabatar min da cikakken sunanka?
Malam Niga: Sunana Lawal Yusuf Maduro da aka fi sani da Malam Niga da ke zaune a Rigasa a garin Kaduna.

Na samu labarin ka sanya gasar cin kofin kwallon kafa, ya abin yake?
Malam Niga: Alhamdulillah, na hada kungiyoyin kwallon kafa kimanin goma sha shida da ke yankin Rigasa ne don su fafata a tsakaninsu a karo na farko.  Mun yi haka ne don kawar da hankalin matasa daga fadawa tarkon yin shaye-shaye da kuma hada kansu don samun dawwamammen zaman lafiya a yankin Rigasa da daukacin Jihar Kaduna da ma kasa baki daya. Shi ne makasudin hada wannan gagarumin gasa da kulob goma sha shida suka fafata. Kuma tun lokacin da aka fara gasar kawo yanzu komai na tafiya a daidai ga shi yanzu an kawo wasan karshe da aka buga a ranar Lahadin da ta gabata.  Kuma Alhamdulillah, mun gayyato al’umma da dama daga bangare daban-daban da suka halarci wasan karshen, inda wasu sun zo da kansu wasu kuma suka turo wakilai kuma Alhamdulillahi kowa ya yaba da kokarin da muka yi game da shirya wannan gasa.  Sannan hatta manyan jiga-jiga gwamnati da Hakimai da Dagatai da jami’an tsaro sun samu halartar bikin rufe gasar inda aka gudanar da wasan karshen lafiya ba tare da wani tashin hankali ba.  Kuma an gudanar da gasar ce a filin wasa na makarantar firamare da Lokoja da ke Rigasa Kaduna, a nan ne kuma aka gudanar da wasan karshen.

Wannan shi ne karon farko da ka fara sanya kofi?
Malam Niga: A gaskiya wannan shi ne karo na farko da na fara sanya kofi a fagen kwallon kafa don matasa su yi gasa a kai.  Sai dai insha Allah ina fata daga wannan karo za mu yi kokarin ganin mun cigaba da irin haka daga lokaci zuwa lokaci.

To kungiyoyin da suka fafata a wannan gasa ta Malam Niga, a yankin Rigasa kawai aka gayyato su ko an hada da na wadansu kananan hukumomin Jihar Kaduna?
Malam Niga:  Gaskiya wannan gasa da yake shi ne somin-tabi mun gayyato kungiyoyin kwallon kafa guda 16 ne kawai daga yankin Rigasa don su fafata.  Sai dai  a gaba za mu yi tunanin fadada abin don gayyato wadansu kungiyoyin kwallon kafa daga wurare daban-daban ba yankin Rigasa kawai ba.  Don haka akwai yiwuwar mu karade daukacin kananan hukumomin Jihar Kaduna guda 23 a gasa ta gabata don ganin mun zakulo zaratan ’yan kwallo biyar-biyar daga kowace karamar hukuma don mu hada su a matsayin kungiyoyin kwallon kafa daban-daban don su fafata.  Yin haka zai kawo cigaba a yankin Rigasa da ma a daukacin Jihar Kaduna inda za a samu damar zakulo zaratan ’yan kwallon da za su wakilci Jihar da ma kasa baki daya.

To ita wannan gasa, wa ke daukar nauyinta?
Malam Niga: Gaskiya ni kadai na dauki nauyinta, hasalima ban samu tallafin wani ko wata kungiya ko gwamnati a game da gudanar da wannan gasa ba.   Ni na dauki nauyinta ta hanyar dan abin da nake samu inda na ware wani kaso don ganin na tallafawa matasa a harkar wasan kwallon kafa a yankin Rigasa.  Kama daga lokacin da aka fara gasar zuwa karshe na kashe makudan kudi, kuma Alhamdulillah tun da an samu nasara.

 Akwai dalibanka a cikin ’yan kwallon da suka fafata a wannan gasa?
Malam Niga: Gaskiya ba wani daga cikin dalibaina da suka fafata a wannan gasa da na shirya a karo na farko.  Sai dai ina yunkurin ganin wannan cibiya mai kula da matasa masu shaye-shaye da miyagun halaye za ta yi kokarin samar da nata kungiyar kwallon kafa da kuma ta sauran wasanni don ganin ana damawa da mu a kowane bangare na wasanni.  Ina sa ran nan gaba kadan za mu yi kokarin samar da haka insha Allah.

Kamar tsawon wane lokaci aka dauka ana gudanar da gasar?
Malam Niga: Mun dauki tsawon watanni biyu zuwa uku ana gudanar da ita.  Kuma abin sha’awa shi ne tun daga lokacin da aka fara gasar daga cikin kungiyoyin 16 da suka fafata, duk kungiyar da aka fitar mun ba ta kyautar kwallo daya a matsayin tagomashi na halartar gasar, kenan babu kungiyar da ta fafata a gasar ba tare da samun kyauta ba.  Mun yi haka ne don karfafa musu gwiwar shiga gasannin da za mu shirya nan gaba.

Wane kira kake da shi ga gwamnati a kan wannan yunkuri naka na hada kan matasa ta hanyar sanya kofin wasan kwallon kafa?
Malam Niga:   Ina kira ga gwamnatin Jihar Kaduna ta shigo ciki don ganin ta tallafa don a kara fadada wannan gasa da muka shiryawa saboda muhimmancinta. Hada kan matasa da samar da zaman lafiya na daga cikin hakkin gwamnati don haka akwai bukatar gwamnati ta shigo ciki don karfafa mana gwiwar fadada abin. Ina addu’ar Allah Ya kawo karshen tashe-tashen hankula da aikata miyagun ayyukan da matasa ke yi ta hanyar gudanar da wannan gasa ta kwallo a yankin Rigasa da ma a Jihar Kaduna baki daya.

Mun gode da ka bamu dama muka zanta da kai.
Malam Niga: Ni ma na gode. Allah Ya kara dauka jaridar Aminiya da kuma ba Jiharmu ta Kaduna da ma kasa baki daya dawwamammen zaman lafiya.