Wani matashi da ke sana’ar daukar hoto a Jihar Legas mai suna Muhammadu Rabi’u Abubakar ya ce alherin da yake samu a sana’arsa ta daukar hoto ya fi wanda ya samu a sana’ar canji.
Muhammdu Rabi’u, dan kimanin shekaru 42, dan asalin garin Raddawa a yankin karamar Hukumar Musawa da ke Jihar Katsina ya yi furucin haka ne yayin yake tattaunawa da Aminiya a makon da ya shige.
Ya ce, “A da ina yin sana’ar canji a kasuwar canji ta filin saukar jiragen sama na Murtala Muhammed da ke Ikeja a Legas, a lokacin ina zaune ne a karkashin Alhaji Ali Zango. Daga bisani da na ga kasuwar ba ta yi mini ba, sai na koma Gashuwa da ke Jihar Yobe. Bayan na shekara guda ina rokon Allah Ya ba ni sana’ar da zan rike a hannuna, sai na yanke shawarar dawowa Legas, sai na fado cikin Abbatuwa, sai tunanin sayen na’urar daukar hoto ta fado mini, sai na saya, na fara daukar hoto kuma na gode wa Allah, domin hankalina ya kwanta ina samun alheri cikin kwanciyar hankali da jin dadi”.
Ya ci gaba da cewa, “Gaskiya babu yadda za a hada sana’ar daukar hoto da canji saboda ita sana’ar canji sana’a ce ta jira. Sai ka jira kwastoman da zai ba ka canji sannan ka samu kudin da za ka ci abinci. Ita kuwa sana’ar daukar hoto babu jira kuma kana zaman kanka ne ba a karkashin wani ba”.
Ya bayyana cewa bai yi nadamar barin sana’ar canji ba, saboda alherin da yake samu a sana’ar daukar hoto.
Muhammadu Rabi’u, wanda ya taba shiga aiki soja, ya ce ya samu nasarori daban-daban a sana’ar daukar hoto da suka hada da yin aure da mallakar shagon daukar hoton.
Ya kara da cewa matsalar da yake samu ita ce ta wulakancin da ma’aikata masu sanya kayan sarki suke yi masa. “kalubalen da na taba fuskanta shi ne wani lokaci na dauki hoton wani mutum, sai wani soja da ke kusa da wurin ya taso ya mare ni. Sai na kai karar sa wurin shugabansu, sai ya hada ni da wani soja muka taho neman sojan da ya mare ni, amma muna zuwa sai muka tarar ya gudu”. Inji shi.
Daga nan sai ya ce yana daukar hotunan jama’a da na bukukuwa da na wasannin gargajiya.
Ya yi kira ga mutane da suke raina sana’ar su daina domin sana’ar ta wuce duk yadda mutane suke tunani wajen samun alheri. “Ina so jama’a su sani cewa sana’ar daukar hoto ba abar rainawa ba ce, sirrinta shi ne ba a yin asara. Ko da ka dauki hoto ba a saya ba, idan ka ajiye shi ba asara ka yi ba. Nan gaba za a iya zuwa a nema a ba ka kudi mai yawa”. Inji shi.
Na samu alheri mai yawa a sana’ar daukar hoto -Rabi’u Maihoto
Wani matashi da ke sana’ar daukar hoto a Jihar Legas mai suna Muhammadu Rabi’u Abubakar ya ce alherin da yake samu a sana’arsa ta daukar…