Ana ta kai-komo da bayanai game da tsarin almajirci a Najeriya. Malam Suleiman Danyaro ya wallafa littafinsa mai sunan: ‘Almajirai Ko Attajirai?’ wanda kirkirarren labari ne, inda a ciki yake ba da labarin wani almajiri wanda tsarin da ya bi ya yi Karatun Allo ya sha bamban da irin wanda yara suke yi a Arewacin Najeriya. A tattaunawarsa da Aminiya, marubucin ya bayyana cewa ya rubuta wannan littafi ne domin ya fadakar da al’umma cewa ba lallai ne sai an tura yara bara ba ake samun ilimi.
Mene ne takaitaccen a tarihinka?
To da farko sunana Suleiman Danyaro. An haife ni a ranar 6-8-1966 a Tudun Wada Kaduna. Tun ina karami aka sa ni a makarantar allo. Sai a 1973 aka sanya ni a makarantar firamare, wacce ke harabar Kwalejin Kimiyya da Kere-Kere ta Kaduna, (Kaduna Polytechnic), a nan Kaduna. Na gama makarantar sakandare ta jeka-ka-dawo da ke Tudun Wada Kaduna, wacce ake kira da Maimuna Gwarzo a 1985.
A bangaren aiki ko sana’a kuwa, na taba dinki da kasuwanci na tsawon shekara bakwai. Bayan haka na koma karatu a Kwalejin Kimiyya da Kere-Kere ta Kaduna, inda na samu shaidar Babbar Diploma (HND) a fannin Al’amuran Kasuwanci. Yanzu haka ina wakiltar kamfanoni biyu na man fetur masu zaman kansu, wato Ango Joint Petroleum da kuma Alkaram Petroleum a Matatar Mai ta Kaduna. Kuna ni ne Sakataren Kudi na Arewa na Kungiyar Kananan Ma’aikatan Man Fetur Masu Zaman Kansu (IMB/NUPENG).
A bangaren iyali, ina da mace daya da ’ya’ya maza da mata.
Yaushe ka fara harkar rubuce-rubuce kuma me ya ja hankalinka ga harkar?
Na fara harkar rubutu kamar shekara 12 da suka wuce, amma sai a shekarar 2015 aka buga min littafina na farko, mai suna ‘Mata Masu Duniya.’ Amma kash, sai bai shiga kasuwa don wasu dalilai. Na shiga harkar rubutu ne don in bayar da tawa ’yar gudunmawar wajen ganowa da ba da shawara a kan wasu abubuwan da ke ci wa al’umar Arewacin kasar nan da ma kasar baki daya tuwo a kwarya.
Zuwa yanzu littattafai nawa ka rubuta, wadanne aka buga suka shiga kasuwa, wadanne ne kuma ba a buga ba?
A yanzu littattafai biyu na wallafa, wanda ya shiga kasuwa shi ne ‘Almajirai Ko Attajirai?’ Wanda kuma bai shiga kasuwa ba shi ne ‘Mata Masu Duniya.’
Littattafai biyu kadai ka rubuta?
Na fara rubuta guda uku amma ban kammala ba, sai nan gaba.
Yanzu ga shi ka fitar da littafin ‘Almajirai Ko Attajirai?’ Ka yI bayani cikakke game da kunshiyarsa kuma me ya sa ka rubuta shi?
Da farko abin da ya sa na rubuta littafin shi ne ganin yadda maganar bara da ’ya’yan Hausawa suke yi da sunan neman ilimin Alkur’ani ta zama wani abin magana a kasar nan. Saboda mutane da yawa suna ganin ya kamata a sauya wannan tsarin don yana cutar da yaran. Sannan babban abin tambaya a nan shi ne, shin dole ne sai yaran sun yi bara? To, ganin haka ne na rubuta littafin domin bayar da misalin yadda za a yi karatun allo ba tare da bara ba.
Kuma a takaice littafin ya kunshi labarin wani yaro ne mai suna Umar Yunusa, wanda daga kauyen Kano aka kai shi birni karatun allo. Da farko ya fara bara amma bai dade ba ya sauya tsarin, yakan yi aikin dako a ranakun Alhamis da Juma’a, ranakun da ba a makararanta. A kan haka shi ne bayan ya haddace Alkur’ani sai kuma ya shiga makarantar boko har ya zama malamin jami’a. A sakamakon nasarar da ya samu ne har Dagacin garinsu ya karrama shi.
A ranar da aka karrama shi, cikin jawabinsa ya kawo shawarar yadda za a rika yin karatun allo ba tare da tura yara birni suna bara ba.
Wadanne kalubale ka fuskanta a matsayinka na marubuci?
Babban kalubalen da na fuskata shi ne wajen mawallafa. A gaskiya na sha wuya a nan, sai da Allah Ya taimake ni aka ba ni shawarar in tafi wurin Alhaji Ado Ahmad Gidan Dabino. To a nan ne fa na ga aiki da cikawa, da fatan Allah Ya saka masa da alheri.
A matsayinka na marubucin da ya fitar da littafi, yaya kake ji a ranka? Shin ka samu biyan bukata, kasancewarka marubuci? Me ka samu na nasara da za ka yi alfahari?
Fitar littafina ya sa ina cike da farin ciki a raina. Sannan maganar biyan bukata, ina nan ina sauraren yadda jama’a za su fahimci littafin tukunna, musamman da yake littafin bai dade da fitowa ba. Babbar nasarar da na fara samu ita ce yadda na ga mutane sun fara murna da ganin littafin.
Bayan fitar littafin, yanzu me kake shirin yi a fagen rubutu?
Ina shirin tura wa mawallafa littafina na gaba, wanda wasan kwaikwayo ne, in Allah Ya yarda.
Al’umma da gwamnati na kokawa kan al’amarin almajirci da bara, ta yaya kake ganin gwamnati za ta samu nasara a wannan batu?
To, ni a ganina cin nasarar gwamnati wajen hana bara ba fa karatun allo ba, ya danganta da irin gudunmawar da ku ’yan jaridar Arewa za ku bayar wajen wayar wa al’umma kai, wajen tantance matsayin irin wannan barar a Musulunce. Misali, ku tambayi malamai, wai shin wannan bara da yaran ke yi sharadi ne a Musulunce sai an yi ta sannan ake samun karatu? Idan sharadi ne, shin kasashe irin su Saudiyya musamman biranen Makka da Madina, inda aka saukar da Alkur’ani, ’ya’yansu suna yin bara a yayin da suke neman ilimi? Kasar Indonesiya da ta fi kowace kasa yawan Musulmi a duniya, shin ’ya’yansu na yin bara? Kasashen Pakistan da Masar fa, suna yi? Idan ba su yi don me? Ko dai abin al’ada ce aka hada ta da addini a kasar Hausa?
Sai mu zo bangare na biyu. Nan ku tambayi masana tarihin kasar Hausa, shin yaushe aka fara al’adar tura yara bara? Tarihi dai ya nuna a 1903 Turawa suka wargaza mafi girman kasuwar bayi a Arewacin Najeriya, wadda take birnin Kano. Sannan shekara biyu kafin nan, Sarkin Kwantagora Ibrahim ya taho da rundunar mayaka zai yaki Zariya, sai Turawa suka shiga tsakani suka hana yakin, kamar yadda yake a wani littafin tarihi mai suna ‘Zuwan Turawa Najeriya ta Arewa.’ Duk wadannan abubuwa biyun sun faru ne a kasa da shekara 120 da suka wuce. To abin tambaya a nan, a wancan lokacin da ake kai hare-hare ana kamo bayi, kasashen Hausa suna yakar junansu, shin akwai sarari ko halin mutum ya tura dansa nesa karatu yana bara don ya ci da kansa? Ko kuwa sai da Turawa suka hana kai hare-hare, hankali ya fara kwantawa tukunna aka samu sukunin kawo tsarin da almajirai ke taruwa daga nesa suna yin noma a gonakin malamansu, suna ciyar da kansu, daga nan kuma sannu a hankali har bara ta shigo ta samu gindin zama kamar yadda ake a yanzu? Sannan kada a manta akwai kabilar Yarabawa a kasar nan kuma akasarinsu Musulmi ne. Kuma yaransu na yin karatun Alkur’ani amma ba su yin bara irin ta yaran Hausawa da Fulani. To, shin akwai wata fa’ida ce da Yarabawa ke rasawa ta rashin yin bara da Hausawa da Fulani ke samu da suka yi wa abin rikon fika, wanda in an yi maganar hana irin wannan barar sai su ji kamar an taba musu wani kayan gado?
Kodayake Hausawan ma ba duka masu karatun allo suke bara ba. Kuma bincike ya nuna, duk inda ka ji an ce ga wani yaro ko yarinya masu shekara bakwai zuwa 12 sun sauke ko sun haddace Alkur’ani, to za ka tarar masu karatu a gaban iyayensu ne, ba masu bara ba. Haka in ka ji an ce ga wani yaro ko yarinya ta yi na daya a gasar karatun Alkur’ani a nan gida Najeriya ko Makka ko Dubai, to kuwa za ka tarar masu karatu a gaban iyayensu ne. To don haka mene ne yake wajabta wa wadansu yaran cewa dole sai an tura su nesa sun yi bara a makarantar allo? A karshe amsar tambayarka ita ce, in dai malamai suka tabbatar da bara ba sharadi ba ne wajen neman ilimin Alkur’ani, to gwamnati za ta iya cin nasara wajen hana wannan al’ada ta bara, ta fito da yadda yara za su rika yin karatun allo a gaban iyayensu, ta yadda za su iya hadawa da karatun zamani, ko koyon wata sana’a. Da fatan Allah Ya sa a kalli al’amarin da nufin yin gyara.