Wata yarinya mai suna A’ishatu Umar, wadda ke da lalurar makanta, ta bayyana ta koyi sana’ar hannu ne saboda tana fatar kasancewa mai dogaro da kanta a duk yanayin da ta samu kanta a rayuwa.
’Yar shekara 20, A’ishah ta kware ne wajen saka zannuwan gado da kujerun zama da kwando da sabulun wanki da jaka da sauransu.
A zantawarta da Aminiya, ta bayyana cewa: “An haife ni a shekarar 1994 a unguwar Kawo da ke Kaduna ba tare da wata lalura ba. Na rasa idanuna ne a lokacin ina da shekara 12 sakamakon wata rashin lafiya da na yi fama da ita. Amma ko bayan da wannan lalurar ta same ni, ba kowa ke fahimtar cewa makauniya ce ni ba, saboda yadda idanuna ba su bambanta daga yadda suke kafin faruwar lalurar ba. Na yi firamare da sakandare cikin dalibai masu gani. Kuma ina da haddar Alkur’ani har zuwa izu 15. A bara ne na je Makarantar Nakasassu ta Jihar Kaduna (Kaduna State Special Education School -KASSES), inda na koyo karatun makafi da ake kira ‘Brailles’ da kuma sana’o’in hannu da dama. Kodayake a yanzu irin wadanan kayyakin da nake sakawa ba sayarwa nake ba saboda yadda iyayena ba su amince da na yi hakan ba.” Inji ta.
Da wakilinmu ya tambaye ta ko me ye sa haka, sai ta ce, “Hakan bai rasa nasaba da yadda suke dauke dukkan nauyin da Allah Ya rataya musu a kaina. Kuma na dage ne kan koyon wadannan sana’o’i saboda in su ne yau, ba su ne gobe ba. Ba fata muke yi ba, amma dai saboda maganin ko-ta-kwana”.
A karshe ta yi fatan ci gaba da karatunta tare da bayyana burinta na zama ’yar jarida, idan ta kammala.
Na koyi sana’a ne don maganin ko-ta-kwana – Makauniya A’ishah
Wata yarinya mai suna A’ishatu Umar, wadda ke da lalurar makanta, ta bayyana ta koyi sana’ar hannu ne saboda tana fatar kasancewa mai dogaro da…