Shugaban kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau ya bayyana cewa ya gaji da bala’in da yake gani a halin yanzu, don haka yana son ya mutu, ya tafi Aljanna. Haka kuma ya ce duk da cewa sojoji sun kore su daga dajin Sambisa, har yanzu suna rike da wasu wurare, duk da cewa bai ambata maboyar tasu ba.
Shekau ya fadi haka ne a ranar Larabar da ta gabata, cikin wani bidiyo na minti goma, wanda Aminiya ta samu gani. “Idan da kun kashe mu, me ya sa har yanzu muke raye?” Abin da ya fada ke nan, yana kalubalantar hukumomin tsaron Najeriya. Ya bayyana cewa yana nan a boye, babu wanda zai iya gano shi, kamar kuma yadda ya yi alkawarin ci gaba da yakinsa na kafa “Daular Musulunci.”
“Na gaji da wannan bala’in, gara in mutu, in tafi Aljanna,” inji Shekau a cikin bidiyon, wanda ba a samu bayanin inda aka dauke shi ba.
A wani labari mai kamar wannan, Sojan Najeriya sun bayyana cewa sun kara samun gagarumar nasara a yakinsu da ’yan Boko Haram, inda a Talatar da ta gabata suka darkaki wasu burbushin ’yan Boko Haram da ke boye a yankin tafkin Chadi da kuma dajin Sambisa, tare da lalata da kwato muhimman makamai da na’urorin sadarwa.
A nasarar da suka samu, kamar yadda Kanar Onyema Nwachukwu, Mataimakin Daraktan Hulda da Jama’a na Shirin Yakin Lafiya Dole ya bayyana, rundunar ta yi nasarar gano boyayyun wuraren da ’yan Boko Haram din ke hada bama-bamai, inda suka yi nasarar kwato makamai da alburusai da motoci da sauran na’urori daban-daban da suke amfani da su.
A yayin wannan aikin, rundunar ta yi nasarar kwato manyan tukwanen gas guda 88 da kwamfutar tafi-da-gidanka guda 1 da Rediyon Sadarwa mai cin zangon mita 100 da sauransu. Haka kuma an lalata masu babura 22 da kekuna 18, kamar kuma yadda aka tarwatsa rumbun ajiyar kayan masarufi guda daya.