Wani fitaccen dan kasuwa da ke sayar da motoci da sauran ababen hawa a Kamfanin Aminchi Motors da ke birnin Gusau a Jihar Zamfara, ya ce kashe-kashe da cire sassan jikin mutane domin ya ci namansu sannan ya sayar da ragowar ga mabukata wani bangare ne na rayuwarsa da a yanzu ya zame masa jiki.
Mutumin mai suna Aminu Baba ya shiga hannun jami’an tsaro na hukumar ’yan sandan Jihar Zamfara a makon da ya gabata, inda ake zargin hannunsa a kisan wani yaro dan shekara 9 da aka yi a Gusau.
- Ina dan wasan da ya zura kwallon da Najeriya ta lashe AFCON 2013, Sunday Mba, yake?
- AFCON: Yadda alkalin wasa ya hura tashi lokaci bai yi ba
Da yake yi wa manema labarai holen wanda ake zargin, Kwamishinan ’Yan sandan Jihar, Mista Ayuba N Elkanah, ya ce mutumin yana da mata har uku da kuma ’ya’ya 19.
Mista Ayuba ya bayyana cewa akwai wasu samari biyu da mutumin ya dauka aikin sato masa kananan yara maza sannan suka kashe su, inda ya ce har sun aikata hakan sau biyu kuma ya biya su Naira miliyan daya a matsayin ladan wannan aiki.
A cewar mutumin da ake zargi, “na biya su Naira dubu 500 a matsayin ladan kashe kowane yaro daya da suka yi.
“Mun cire mazakutar yaran, idanu, ’ya’yan hanjinsu da makoshi, kuma na kan ci wadannan sassan jiki sannan na sayar da ragowar ga masu bukata,” a cewarsa.
Sai dai mutumin bai ce uffan ba a kan hanyar da yake samun kudin biyan ladan wannan aika-aika, sannan ya ki bayyana cewa ko yana da wadansu abokanan hulda da suke aikata wannan mummunar ta’ada tare.
Kwamishinan ’yan sandan ya ce daya mutumin da ake zargi da ya shiga hannu mai suna Abdulshakur Muhammad, ya shaida musu cewa wannan shi ne karo na uku da Aminu Baba ke ba shi aikin fataucin sassan jikin mutane, kuma kowane aiki yana biyansa ladan Naira dubu 500, kuma ya samu nasara wajen aikata hakan har sau biyu kafin dubunsa ta cika.
Abdulshakur ya ce suna aiki ne tare da wani Abdullahi Baba da Ahmad Tukur wadanda suke taya shi yaudarar kananan yaran maza su kai su kangwaye, inda a nan suke kashe su sannan su yanki ’ya’yan hanji, makoshi, mazakuta da kuma idanu biyu wadanda suke kai wa Aminu suka karbi ladansu na Naira dubu dari biyar kamar yadda suka kulla yarjejeniya da shi.
Aminiya ta ruwaito cewa, tun makonni biyu da suka gabata ne aka tsinci gawar wani yaro dan shekara 9 mai suna Ahmad Yakubu Aliyu a cikin wani kango da ke Unguwar Barakallahu a birnin na Gusau.
Bayanai sun ce an nemi yaron ne an rasa bayan tasowarsu daga makarantar Islamiyya da ke unguwar Gadar Baga, inda bayan wasu kwanaki mai wannan kango ya yi kicibus da gawar yaron har ta fara rubewa yayin da ya kai ziyara kangon domin ci gaba da aikin gini.
Nan take ya ankarar da ’yan sanda a kan lamarin wanda suka tabbatar cewa an cire ’ya’yan hanjin yaron sannan an rufe kansa a cikin wata leda.