Hajiya Bilkisu Yakubu Indabo ita ce Shugabar Riko ta Karamar Hukumar Wudil a Jihar Kano, ita ce kaɗai mace a cikin kantomomin da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya nada.
A ganawarta da Aminiya, Bilkisu Indabo wacce kwararriyar ma’aikaciyar lafiya ce, ta ce naɗin nata zai buɗe wa mata kofa su iya tsayawa takarar mukamai a matakai daban-daban da sa su a cikin harkokin mulki a jihar baki ɗaya.
Mene ne tarihinki a takaice?
An haife ni a Indabo a Karamar Hukumar Wudil.
Bayan kammala karatun firamare da sakandare na tafi Makarantar Kula da Aikin Tsafta ta Kano inda na yi Difiloma a kan tsaftar muhalli daga nan na samu aiki a Karamar Hukumar Wudil.
- Taurarin Zamani: Sadiq Muhammad Yelwa (Ɗan Gwamna)
- An haramta fina-finai na faɗan daba da harkar daudu a Kano
Saboda sha’awata ga aiki a asibiti saboda in taimaki al’umma ta sa na zaɓi karatun lafiya, inda na je Kwalejin Koyon Aikin Jinya ta Kano wadda na kammala a shekarar 2012 daga nan na samu aiki a Asibitin Muhammad Abdullahi Wase da ke Nasarawa a Kano.
Haka kuma ina ɗaya daga cikin waɗanda suka ci gajiyar tallafin karatu na kai ɗalibai kasashen waje na tsohon Gwamna Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso, inda na yi karatun digiri a fannin jinya a Jami’ar Masoura da ke kasar Masar kuma na kammala da mai daraja ta ɗaya kuma a Masar na samu dama inda na je Kwalejin Tarbiyya na karanci harshen Larabci, bayan kammala karatuna na dawo na ci gaba da aikina a Asibitin Nasarawa.
Daga baya an tura mu Jami’ar Bayero domin karanta Babbar Difloma ta Ilimi domin koyarwa bayan mun kammala aka tura ni Kwalejin Koyon Aikin Jinya ta Kano domin in koyar.
Na sake samun dama lokacin da muka sake samun tallafin karatu na Injiniya Rabi’u Kwankwaso inda aka tura ni kasar Indiya na yi digiri na biyu a fannin jinya.
Yaya kike kallon wannan mukami naki na Shugabar Karamar Hukuma?
Ina ganin an sa kwarya a gurbinta, kuma babban abu ne na ’yanta mata kuma zai nuna cewa bai wa mata dama abu ne mai kyau.
Kuma za mu dauki wannan mukami cewa an yaba wa mata kokarin da suke yi lokacin kamfe da zabe.
Wannan ba yana nuna cewa za mu yi abin da maza za su yi ba ne, dama ce ta mu taimaki mata da matasa da kananan yara kuma mu karfafi maza gaba daya.
Bayan haka a wannan karamar hukumar akwai maza da dama da za su iya rike wannan mukami, amma tunda ni Allah Ya kaddarawa, ina kira ga daukacin jama’ar wannan karamar hukuma su zo su taimaka mana su ba mu goyon baya domin mu ci da karamar hukumarmu gaba.
Ta wace hanya kike gani za ki iya kawo canjin da ake bukata a rayuwar mata a wannan karamar hukuma?
Ina da tabbacin za mu kawo canji mai kyau, gudunmawar mata da goyon baya da suka ba mu ba za mu manta ba, za mu saka musu.
Shugabancinmu zai kula da tallafa wa mata da yara wajen ilimantar da su da sama musu kayan more rayuwa.
Wane kira za ki wa mata?
Haƙiƙa za mu tabbatar mun yi adalci a wannan shugabanci, musamman a matsayina na mace zan yi duk mai yiwuwa wajen ganin mun taimaka wa mata. Kuma ina kira gare su da su kula da karatun ’ya’yansu maza da mata.
Shin kina tunanin takara a nan gaba?
Gaskiya ban taba tunanin zan samu wannan mukami ba a rayuwata saboda akwai mutane da dama da suka fi ni cancanta, amma haka Allah Ya kaddara min.
Don haka ban san me zai faru gobe ba, amma a yanzu an ba ni aiki kuma shi ne a gabana kuma shi zan mai da hankalina a kai kuma zan yi iyakar kokarina.