✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

N-Power da GEEP: An kara yawan masu samu zuwa miliyan daya-daya

Gwamnatin Tarayya ta kara yawan matansa da za a rika dauka a shirin aikin tallafin N-Power zuwa miliyan daya. Da yake sanar da haka, Shugaba…

Gwamnatin Tarayya ta kara yawan matansa da za a rika dauka a shirin aikin tallafin N-Power zuwa miliyan daya.

Da yake sanar da haka, Shugaba Muhammadu Buhariya ya ce gwamnatin ta kuma fadada shirin tallafa wa sana’o’i na GEEP ta yadda mutum miliyan za su amfana a nan gaba.

Yadda rashin tsaro ya sa ’yan Arewa dawowa daga rakiyar Buhari

Ganduje ya yi ta’aziyyar mutanen Dambatta 16 da aka harbe

“A shirinmu na fitar da ’yan Najeriya miliyan 100 daga kangin talauci, na ba da izinin kara yawan masu cin gajiyar shirye-shiryenmu na tallafin inganta rayuwa.

“An ninka yawan masu cin gajiyar shrin N-Power zuwa mutum miliyan daya; haka kuma mutum miliyan ne za su ci gajiyar shirin GEEP”, inji Buhari.

A sakon da ya wallafa ta shafinsa na Twitter, Buhari ya kara da cewa, “’yan makarantar firamare miliyan biyar ne a fadin Najeriya za su ci gajiyar shirin gwamnati na ciyarwa a makarantu”.

Ya bayyana hakan ne yammacin Alhamis 10 ga watan Disamba, 2020.