Bayan mutuwar akalla mutum 35, Gwamnatin Najeriya za ta tsunduma wajen gudanar da allurar rigakafin cutar shawara a jihar Delta da ke Kudancin kasar.
Hukumar Lafiya a matakin farko NPHCDA ce ta sanar da hakan a ranar Asabar da ta gabata.
- Ta gutsure mazakutarsa bayan ya yi mata fyade
- Ma’aikatan lafiya sun gindaya sharadin janye yajin aiki
Sanarwar da Hukumar NPHCDA ta fitar ta ce za a gudanar da rigakafin ne tare da hadin gwiwar Gwamnatin jihar Delta a karkashin kulawarta.
Binciken da mahukuntan lafiya suka gudanar ya nuna cewa cutar shawara ce ta ke kassara mutanen wadda a harshen Ingilishi ake kira Yellow Fever.
Tun a ranar 24 ga watan Yulin ne aka samu rahoton mutum na farko da ya mutu a sakamakon kamuwa da wata bakuwar cutar wadda daga bisani bincike ya nuna cewa cutar shawara ce.
Wata sanarwa da Kwamishinan lafiya na jihar Mordi Ononye ya fitar a ranar Juma’ar da ta gabata ta ce cutar ta kasha mutane da dama musamman matasa ’yan tsakanin shekara 18 zuwa 25 a karamar hukumar Ika ta Arewa maso Gabas.
Kazalika Kwamishina lafiya na jihar Enugu, Dokta Ikechukwu Obi a ranar Asabar ya ce mace-macen da ake samu a jihar a baya-bayan nan na da alaka ne da cutar shawara.
Kwamishinan ya ce an samu mutuwar kusan mutum 57 a yankunan Ette Uno da Umuopu da ke garin Ezike a karamar hukumar Igbo-Eze ta Arewa a jihar.