✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamna da jiga-jigan siyasa a Delta sun fice daga PDP zuwa APC

Ba zai yiwu mu ci gaba da tafiya a jirgin da zai nutsar da mu ba.

Gwamnan Delta, Sheriff Oborevwori da wasu jiga-jigan ‘yan siyasa na jihar sun sun sauya sheƙa daga jam’iyyar PDP zuwa APC.

Daga cikin jiga-jigan da suka sauya sheƙa har da tsohon gwamna Ifeanyi Okowa, shugaban jam’iyya, da sauran masu ruwa da tsakin jam’iyyar reshen jihar.

Sanarwar ficewar ta su ta zo ne bayan kammala taron sa’o’i shida da suka gudanar a gidan gwamnatin jihar, kamar yadda sanarwar da Sanata daga jam’iyyar, James Manager, ya bayyana.

“Duk wani dan PDP na jihar har da gwamna, da tsohon gwamna Okowa, da shugaban majalisa, da shugaban jam’iyyar, da duk ciyamomin ƙanannan hukumomi mun amince mu fice mu koma APC.

“Ba zai yiwu mu ci gaba da tafiya a jirgin da zai nutsar da mu ba,” in ji Sanata James Manager.

A nasa ɓangaren, kwamishinan yada labaran gwamnan, Aniagwu Charles, ya tabbatar da ficewar gwamnan da ma sauran jagorori da masu ruwa da tsakin PDP.