Gwamnan jihar Abia Okezie Ikpeazu ya killace kansa saboda fargabar bullar cutar COVID-19 a fadar gwamnatin jihar.
Gwamna Ikpeazu da mataimakinsa Ude Oko Chukwu da sauran ‘yan Majalisar Zartarwar jihar na killace kansu ne bayan iyalen jagoran yaki da cutar COVID-19 a jihar Marigayi Solomon Ogunji sun kamu da ita.
Mista Ogunji shi ne kuma kwamishinan muhalli na jihar.
Ya rasu ne a makon jiya sakamakon rashin lafiya mai nasaba da hawan jini, a cewar Kwamishinan Yada Labaran jihar Chief John Okiyi Kalu.
Raswuar Mista Ogunji ta sanya fargaba yiwuwar cutar coronavirus ce ta yi ajalinsa.
- COVID-19: Za a kafa cibiyoyin killace majinyata a dukkan jihohi
- Coronavirus: An sallami ragowar masu cutar a Kebbi
Hakan ce ta sa aka dauki jinin iyalen mamacin domin yi musu gwajin cutar.
Sakamakon gwajin da ke nuna iyalen mamacin sun kamu da cutar na ci gaba da haddasa damuwa.
Gwamna Ikeazu da ‘yan Majalisar Zartaswarsa da ‘yan kwamitin ministoci da wadanda suka yi mu’amala da Ogunji za su kasance a killace na tsawon sati biyu.
Kwamishinan Yada Labaran jihar ya kara da cewa gwamnan ya umurci dukkannin wadanda suka yi mu’amala da mamacin da su gabatar da kansu domin a yi musu gwajin cutar.
Kafin yanzu mutum biyar ne kacal suka kamu da coronavirus a jihar Abia.
Daga cikinsu mutum biyu da suka fara kamuwa sun warke.