Shugaban Amurka, Joe Biden, ya janye ƙudirinsa na shiga zaɓen shugaban ƙasar da za a yi a watan Nuwamba.
Wannan na ɗauke ne cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar.
- Gagdi ya gwangwaje ’yarsa da mota bayan ta kammala sakandare
- Hisbah ta lalata barasar N60m a Katsina
Biden, ya ce yana da muradin neman sake tsayawa takara shugaban ƙasar, amma ya ce ya ɗauki matakin ne don kare muradin jam’iyyarsa da kuma ƙasarsa.
Biden ya ci gaba da fuskantar sabon matsin lamba kan haƙura da takararsa, bayan gwaji ya tabbatar yana ɗauke da cutar COVID-19.
A ranar Laraba ne fadar gwamnatin ƙasar ta fitar da sanarwar cewa shugaban mai shekara 81, ya nuna alamun cutar.
Sakatariyar yaɗa labaran shugaban, Karine Jean-Pierre, ta ce an yi wa shugaban rigakafi kuma yana samun sauƙi.
Ta ce shugaban ya killace kansa a gidansa da ke Delaware yayin da zai ci gaba da gudanar da ayyukansa ofishinsa daga gida.
Likitan Joe Biden, Kevin O’Connor, ya ce shugaban na fama da matsalar numfashi da zubar majina da tari, amma ya ce tuni ya fara shan magani.
Daga baya shugaban ya gode wa jama’a kan fatan alheri da suke masa a shafinsa na X (Twitter).
Sau biyu dai a baya ana tabbatar da shugaban na kamuwa da cutar COVID-19.