Ana zargin wani dan kasar China da halaka wata budurwa saboda kin amincewa da tayin soyayyarsa a Jihar Abia da ke kudancin Najeriya.
Budurwar dai ma’aikaciya ce a wani kamfanin sarrafa karafa a Umuahala-Obuzor da ke karamar hukumar Ukwa ta Yamma a jihar Abia.
Ana zargin cewa dan kasar Chinan ya nace da bayyana soyayyarsa a gare ta amma ta bijire wa bukatarsa, ta ki amincewa.
Dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar, Ukwa Gabas/Ukwa ta Yamma a jihar Abia, Chris Nkwonta, ya ce budurwar ta rasu ne sakamakon turo ta kasa da dan Chinan ya yi daga injin mika kayan aiki sama saboda ta ki amincewa da soyayyarsa.
- Direba ya take soja har lahira a Legas
- Manufofin Gwamnatin Tinubu ne silar taɓarɓarewar rayuwa a Najeriya —ACF
Wanda ake zargin ya yi ikirarin cewa ya kashe wa budurwar tasa har Naira miliyan 60 a cikin shekaru biyu, sai kawai aka wayi gari ta yi watsi da shi.
Dan majalisar ya ce an san al’ummarsa da zaman lafiya da mutunta juna, don haka yana rokon hukuma su yi adalci kan wannan batu.