Fassarar Salihu Makera
Godiya ta tabbata ga Allah, muna gode maSa, muna neman taimakonSa, muna neman gafararSa, muna tuba gare Shi. Muna neman tsarin Allah daga sharrukan kawunanmu da munanan ayyukanmu, wanda Allah Ya shiryar babu mai batar da shi, wanda kuma Ya batar babu mai shiryar da shi.
Godiya ta tabbata ga Allah Wanda ya hana tabbata ga bayi ta hanyar mutuwa, kuma Ya hukunta wa kanSa tabbata. Allah Ya ce: “Dukan wanda ke kanta (kasa) mai karewa ne. Kuma abin yardar UbangijinKa Mai girman Jalala da karimci, shi ne yake wanzuwa.”
Na shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Shi kadai Yake ba Ya da abokin tarayya Rayayye, Mai tsayuwa da komai. Kuma na shaida shugabanmu, masoyinmu, abin koyinmu, abin muradinmu, Muhammad (SAW) bawanSa ne kuma ManzonSa, mai gargadi da bushara. Ya isar da sako, ya bayar da amana kuma ya yi nasiha ga al’umma, ya fitar da ita daga duffan jahilci zuwa ga fagen ilimi da haske.
Ya Ubangiji! Ka kara tsira a kan sirrin mai mutuwa a cikin sirrin mai mutuwa da sirrin mai mutuwa da aminci a kan hasken mai mutuwa da cikin hasken mai mutuwa da hasken mai mutuwa, tsira da aminci masu tabbata masu lizimta har zuwa lokacin da mala’ikan Allah mai karbar rai ke raye.
Ya bayin Allah! Ku ji tsoron Allah matukar jin tsoronSa kada ku yarda ku mutu face kuna Musulmi. Ya bayin Allah! Ina yi muku wasiyya da ni kaina da bin Allah da takawa, domin takawa ita ce guzuri a duniya da Lahira, da ita ake tsira a ranar girgiza, ranar da dukiya ba ta amfani balle ’ya’ya, sai wanda ya je wa Allah da zuciya kubutacciya. Ya bayin Allah! Hudubarmu ta yau za mu dubi batun “Mutuwa ce.”
Mutuwa ita ce karewa ko gushewa. Mutuwa mai rusa jin dadi ce, mutuwa kishiyar rayuwa ce. Mutuwa ita ce tashin ruhi zuwa sama da shigar gangar jiki cikin kasa. Bayin Allah! Mutuwa alheri ne ga dukan halitta. Mutuwa kofa ce ta yin hisabi da ukuba. Mutuwa kofar Aljanna ce ko wuta! Kuma mutuwa ita ce bambancin da ke tsakanin Mahalicci da abin halitta. Mutuwa ita ce mai raba tsakanin jama’a. Mutuwa cikar alkawari ne da wa’adi daga Allah. Mutuwa wa’azi ne cikakke. Mutuwa ita ce ke tsara rayuwa, kuma mutuwa tunatarwa ce ga rayayyu. Allah Madaukaki Ya ce: (Allah) Wanda gudanar da mulki yake hannunSa (ikonSa), Ya tsarkaka, kuma Shi Mai iko ne a kan komai. Shi ne Wanda Ya halitta mutuwa da rayuwa domin Ya jarraba ku, Ya nuna wane ne daga cikinku ya fi kyawun aiki.”
Allah Ya halicci bayi ne domin su tsarkake shi da ibada, kuma Ya halicci dare da yini Ya sanya su taskokin adana ayyuka Ya kebance wa bawa abin da ke gare shi da abin da ya wajaba a kansa. Allah Madaukaki Ya ce: “(Mutum) Ba ya furuci da wata magana face a like da shi akwai mai tsaro halartacce.” Kuma Ya ce: “Kowane abu Mun kididdige shi a cikin wani Littafi Mai girma.”
Ku sani ya ku bayin Allah! Lallai wannan duniya gona ce ta shukar da za a girba a Lahira, masu takawa suna rabauta a cikinta, gafalallu kuma suna hasara a cikinta. Yana daga cikin hikimarSa Madaukaki cewa lallai Shi bai sanya wannan duniya a matsayin gidan tabbata da dogewa ba, iyaka Ya sanya ta gidan wucewa da abin lura. Don haka wanda ya ci riba shi ne wanda ya inganta nomansa a cikinta, hasararre kuma shi ne wanda ya bata amfanin gonarsa. Dukan mutane sun san wannan duniya ba wurin zama ba ne ga wani mai rai. Ita mai saurin gushewa ce, mai gaggawar tashi.
Allah Madaukaki Ya ce da AnnabinSa Amintacce duk da yawan so da kaunar da Yake masa: “Ba mu sanya wa wani mutum a gabaninka tabbata ba, shi idan ka mutu, su masu tabbata ne?” Tabbata ta Allah ce Shi kadai Mai karfi. Allah Madaukaki Ya ce: “A wannan rana tasu za a bijiro da su, babu wani abu daga cikinsu da zai boye ga Allah. Mulki na wane ne a ranar? Na Allah ne Makadaici Mai tankwarawa. A wannan rana ana saka wa kowane rai da abin da ya aikata babu zalunci a ranar. Lallai ne Allah Mai gaggawan hisabi ne.”
Muslim ya ruwaito a cikin sahihinsa daga Hadisin Abdullahi dan Umar (Allah Ya yarda da su) ya ce: “Manzon Allah (SAW) ya ce: “Allah zai nade sammai a Ranar Alkiyama, sannan Ya rike su da hannunSa na dama, sannan ya ce: “Ni ne Mai mulkin, ina jabbarai da masu girman kai? Sannan Ya nade kassai da hannunSa na hagu, sannan Ya ce: “Ni ne Mai mulkin! Ina jabbarai da mutakabbirai?”
Wani mawaki ya ce:
“Ka yi guzuri da takawa domin ba ka san, Idan dare ya yi duhu shin za ka rayu zuwa alfijir ba.
Da yawa saurayi kan yi yammaci ya wayi gari yana dariya,
Alhali an kintsa likkafininsa bai sani ba.
Yaro nawa ake sa ran doguwar rayuwarsa, Alhali an shigar da jikinsa a duhun kabari.
Amare nawa ne suka yi ado don angwayensu,
Amma aka karbi rayukansu a daren amarci.
Kuma mai lafiya nawa ya mutu ba tare da cuta ba,
Kuma marar lafiya nawa ne ya rayu na dogon zamani?
Duk wanda ya shekara dubu ko dubu biyu lalli shi,
Babu makawa akwai ranar da zai wuce kabari.”
Allah Madaukaki Ya ce: “Kowane abu mai gushewa ne face Ubangijinka, hukunci nasa ne kuma gare shi ake komawa.”
Lahaula wala kuwwata illah billahi aliyil azim.
Huduba ta Biyu:
Godiya ta tabbata ga Allah Mai kashewa Mai rayawa Wanda Ya ce: “Kowane rai mai dandanar mutuwa ne.” Na shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Shi, kuma lallai Annabi Muhammad BawanSa ne kuma ManzonSa ne.
Ya bayin Allah! Allah Madaukaki Ya hukunta mutuwa a kan kowane mai rai: “Dukan wanda ke kanta (kasa) mai karewa ne. Kuma UbangijinKa Mai girman Jalala da karimci, shi ne yake wanzuwa.” Kowane rai ba makawa ya dandani mutuwa karami ne ko babba, mai mulki ne ko talaka, minista ne ko makaskanci. “Kowane rai mai dandanar mutuwa ne, sannan zuwa gare Mu ake mayar da ku.”
Ya bayin Allah! Mutum bai san yaushe ajali zai auko masa ba, babu kuma wanda yake da karfi ko buwayar ya mutu, haka babu dangin da za su kare shi daga mutuwar da za ta zo masa afke, yana da cikakkiyar lafiya da karfinsa da jin dadinsa da karuwar ni’imarsa da jin dadin rayuwa.
Don haka yana daga cikin gafala mutum ya rika sakaci da batun mutuwa ya kasa kintsa mata har ya yi wasa da wajibai ya auka wa miyagun ayyuka, yana danne hakkokin mutane ba da hakki ba, sai bisa zalunci da yaudara da karya, ya rika ta’adda a kan dukiya ko mutunci ko rai. Yana cutar da Musulmi da makwabtansu, yana karbar hakkokin ma’aikata da masu hidima, ya zalunci matarsa da ’ya’yansa. Ya ku bayin Allah! Mutum nawa ne ya mance da mutuwa ba ya ma tunaninta a zuciya? A’a sai ka gan shi cikin kamalar halinsa yana mai koshin lafiya da nishadi da lafiyar jiki ga kuma dukiya.
Wani ya rera cewa:
“Lallai Yana da bayi masu hankali,
Sun saki duniya sun ji tsoron fitina.
Sun kalle ta kuma lokacin da suka san, Cewa ita ba gidan zama ga mai rai ba ne.
Sai suka sanya ta hanyar wucewa suka rike, Ayyuka na kwarai a cikinta a matsayin hanya.” Allah Madaukaki Ya ce: “Ka ce, “Ya ku wadanda suka tuba (Yahudu)! Idan kun riya cewa lallai ku ne zababbun Allah ba sauran mutane ba, sai ku yi gurin mutuwa idan kun kasance masu gaskiya. Kuma ba za su yi gurinta ba har abada saboda abin da hannayensu suka gabatar. Kuma Allah ne Masani ga azzalumai. Ka ce: “Lallai mutuwar nan da kuke gudu daga gare ta, to, lallai ita mai haduwa da ku ne sannan ana mayar da ku zuwa ga Masanin fake da bayyane, domin Ya ba ku labari ga abin da kuka kasance kuna aikatawa.” Ya bayin Allah! Ku sani lallai mutuwa tana zuwa ne bagatatan, kuma kabari yana gaskata aiki.
“Lallai Allah Yana umarni da adalci da kyautatawa da kuma ba abokin zumunta hakkinsa, kuma Yana hani daga alfasha da abin ki da rarraba kan mutane. Yana yi muku wa’azi tsammaninku za ku yi tunani.”
Imam Sharafudeen Abdussalam Aliagan shi ne Babban Limamin Masallaicn NASFAT na Kasa da ke Abuja, kuma za a iya samunsa
ta tarho mai lamba: 080347108620