Mutumin da ya kitsa ya kuma jagoranci sace dalibai 300 a Makarantar Sakandaren da ke Kankara a Jihar Katsina, Auwalu Daudawa, ya sake daukar makamai, kasa da wata uku bayan ya bayyana tubarsa.
Majiyar Aminiya da ke da kusanci da shi sun tabbatar mata cewa a ranar Litinin ne ya kwashe iyalansa da wasu yaranasa suka koma Dajin Jaja da ke Karamar Hukumar Zurmi a Jihar Zamfara.
- Bayan cika baki, minitsa ya kasa gyara wutar lantarki
- Dole a yi asusun musamman don yakar ta’addanci
- Yadda gwamna ya tunzura mu muka sace daliban Kankara —Auwal Daudawa
- Yadda ake sayen burodi, haka muke sayen makamai —Daudawa
“Ya kira wani mutuminsa a Gusau ya shaida masa cewa ya riga ya sauka a daji kuma ya yanke shawarar sake daukar makamai. Amma babu wanda ya sanar kafin tafiyar tasa,” inji majiyar.
An ruwaito shi yana zargin Gwamnatin Zamfara da rashin tattuanawa da shi yadda ya kamata bayan ya ajiye makamansa.
Kasa da wata biyu bayan ya jagoranci sace daliban a watan Disamban 2202 ne ya fito ya sanar cewa shi da ayyukan ta’addanci har abada, ya kuma mika wa Gwamnatin Zamfara bindigogi 20 da rokoki da sauransu.
Amma, wata uku bayan bayan nan, Daudawa ya yi tubar muzurun tare da komawa dajin da ke kusa da Jihar ta Katsina ne kimanin wata uku bayan ya bayyana tubarsa ga Gwamnatin Jihar Zamfara.
Koma-baya ga Gwamnatin Matawalle
Idan ba a manta ba, Aminiya ta kawo muku hira ta musamman da shi, inda ya ke cewa ko hukunci kisa gwamnati za ta yanke masa a shirye yake, saboda ya yi nadamar abin da ya aikata a baya.
Ya kuma shaida wa Aminiya cewa zai taimaka wa Gwamnatin Zamfara domin ganin tsoffin abokansa ’yan bindiga sun ajiye makamansu.
Bayan tubar Daudawa da manyan yaransa, an ba su masauki ne a gidan gwamnati na tsawon makonni, daga baya aka ba shi gida a wajen garin Gusau, inda shi da iyalansa suka koma da zama.
“Gwamnati ke kula da shi, ban me yake so ba. Ba mamaki ba a biya masu bukatun da yake tsammani ba ne,” inji wata majiya a Gusau.
Masu sharhi sun bayyana tayar da tubar tasa a matsayin koma-baya ga shirin zaman lafiya mai cike da sarkakiya da Gwamnatin Bello Matawalle ta Jihar Zamfara take yi da ’yan bindiga.
Tubabbun ’yan bindiga za su koma daji
Wani gawurtaccen dan bindiga a Jihar ta Zamfara, Shehu Rekeb, ya shaida wa wakilinmu cewa wasu tubabbun ’yan bindiga za su koma daji saboda gudun kai musu hari.
Shehu Kereb ya zargi gwamnati ta yin kumbiya-kumbiya wurin tattaunawa da ’yan bindiga Fulani.
Wani babban jami’in tsaro ya shaida mana cewa tun asali, an yi hasashen cewa shirin zaman lafiyar ba zai dade ba, saboda tun farko ba a gina shi a kan yadda zai dore ba.
“Gaskiya shirin na da matsala saboda ba ba yin yarjejeniyar zaman lafiya ba tare da gindaya sharudda da kuma yin komai a rubuce ba,” inji ta.
Ta kuma koka cewa ba a tanadar wa tubabbun ’yan bindiga wani tsari na bayar da shawarwari da sauya tunaninsu ba, wanda ta bayyana cewa ba su kudade ba zai taba maye gurbin irin wannan tsarin ba.
Tun bayan zuwan Gwamnatin Matawalle a Jihar a shekarar 2019 ta dawo da shirin sulhu da matasan Fulani da suka dauki makamai domin ganin sun ajiye makaman.