✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Mutumin da aka kama da katin zabe 101 zai shekara daya a kurkuku’

INEC ta ce nan gaba kadan za a gurfanar da sauran mutanen da aka kama da tarin katunan zaben a gaban kotu.

Hukumar Zabe ta Kasa INEC, ta ce Kotun Majistare da ke Jihar Sakkwato ta yanke wa wani mutum mai suna Nasiru Idris da aka kama da tarin katin zabe 101 hukuncin daurin shekara guda a gidan yari.

A wani sako da hukumar ta wallafa a shafinta ta Tuwita, ta ce a ’yan makonnin da suka gabata jami’an ’yan sanda sun kama mutane a wurare daban-daban a fadin kasar dauke da katunan zabe masu yawa.

Ta ce a daya daga cikinsu ne ’yan sanda suka kammala bincike a kansa tare da gurfanar da shi a gaban kotu, inda kuma kotun ta yanke masa wannan hukunci

Haka kuma INEC ta ce nan gaba kadan ne za a gurfanar da mutanen da aka kama da tarin katunan zaben a gaban kotu domin su fuskanci hukunci.

A cikin sanarwar hukumar ta ce za ta yi taron wayar da kai da duka kwamishinonin zabe na jijohi 36 na fadin kasar daga ranar 28 ga watan Nuwamba zuwa biyu ga watan Disamba.

A karshen ganawar ne hukumar za ta sanar da ranakun da za ta fara raba katunan zabe a fadin kasar.

INEC ta kuma yaba wa ’yan kasar bisa hakuri da fahimta da suka nuna, musamman ga wadanda ke bukatar a sauya musu katunan da wadanda ke son a sauya musu wurin rajistar