Gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri, ya tabbatar da samun mutum na farko da aka tabbatar ya kamu da cutar coronavirus.
Gwamnan ya tabbatar da faruwar hakan ne bayan sakamakon gwajin da aka yi wa mai dauke da cutar ya fito.
Gwamna Fintiri ya ce akwai mutum hudu wadanda ake zargin suna dauke da cutar, amma bayan sakamakon gwaji ya fito aka ga ba su da ita, don haka aka salleme su.
Ya kara da cewa a ranar 20 ga watan Afrilu aka turo sakamakon gwajin wanda aka tabbatar ya kamu da cutar da na wasu mutum uku.
Mai dauke da cutar dai ya dawo daga jihar Kano ne a makon da ya gabata.
Bayan da ya ga alamomin cutar ne ya killace kansa a gida sannan ya nemi Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Najeriya (NCDC) a waya inda suka je da shi Asibitin Kwararru da ke Adamawa bayan gwajin aka gano yana dauke da cutar.
Gwamna Fintiri ya bukaci jama’a da kada su tayar da hankalinsu, inda ya tabbatar musu da cewa kwamitin yaki da cutar coronavirus na aiki tukuru don ganin an hana yaduwar ta a jihar.
“Nan ba da jimawa ba zan yi jawabi a kan rufe jihar baki daya sannan yaki da cutar coronavirus yaki ne da yake bukatar nasara”, inji gwamnan.