✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mutum miliyan daya za su yi aikin Hajji a bana —Saudiyya

A shekarar da ta gabata, ’yan kasar dubu 60 ne kadai suka yi aikin Hajjin.

Gwamnatin Saudiyya ta sanar da cewa za ta bai wa mutum miliyan daya damar gudanar da aikin Hajjin bana da zai gudana a watan Yuli.

Wannan ne dai adadi mafi yawa da kasar ta bari su yi aikin Hajji tun bayan bullar annobar Coronavirus a shekarar 2020.

Kafar yada labarai ta Aljazeera ta ruwaito cewa, Ma’aikatar Kula da Aikin Hajji da Umara ta Saudiyyan na cewa dole mahajjatan da za su je aikin Hajjin na bana su kasance ’yan kasa da shekara 65, kuma dole sai an yi musu cikakkiyar allurar riga-kafi ta cutar Coronavirus.

A shekarar da ta gabata, ’yan kasar dubu 60 ne kadai suka yi aikin Hajjin.

A shekarun baya kafin bullar Coroavirus, Musulmi daga sassan duniya kusan miliyan biyu da rabi ne ke aikin Hajjin duk shekara.

Aikin Hajji dai gudana daga cikin rukunai biyar na addinin Islama, wanda Allah Ya wajabta shi ga duk musulmin da ya samu iko.