Hukumar Kula da Harkokin Sadarwar Najeriya NCC ta ce masu amfani da wayar hannu a Najeriya yanzu sun kai kimanin miliyan 148 a watan Fabrailu.
Wannan ya nuna cewa an samu kari ke nan bisa wadanda kididdigar ta nuna a watan Janairu na miliyan 147, kusan karin kimanin miliyan daya ke nan.
Hukumar ce ta sanar da hakan a irin bayanan da take sakawa a yanar gizo, kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito.