Hukumar Kula da Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya (WFP), ta yi gargadin cewa akwai kimanin mutum miliyan 13 da ke fuskantar barazanar tsananin yunwa saboda farin da aka fuskanta a sassa da dama na nahiyar Afirka.
Hukumar dai ta ce farin da aka fuskanta sakamakon karancin ruwan sama da aka fuskanta a shekara uku a jere na matukar barzana ga nahiyar.
- Austin Eguavoen zai ci gaba da kasancewa kocin Super Eagles —NFF
- Jamhuriyyar Benin ta tsawaita wa’adin tsare Sunday Igboho da wata shida
A cikin wata sanarwa da Daraktan hukumar da ke Gabashin Afirka, Michael Dunford ya fitar ranar Talata, hukumar ta ce, “Karancin ruwan ya kawo cikas a bangarori da dama, dabbobi na mutuwa, yunwa na karuwa sannan fari na dada kunno kai.
“Lamarin na bukatar a kawo daukin gaggawa da kuma kai tallafi a kai a kai don taimaka wa iyalai da dama.”
Daukewar ruwan sama kafin lokacin da aka saba gani a kasashen Afirka da dama dai da kuma tashin farashin gwauron zabin da kayan abinci da na sauran masarufi ke yi da kuma raguwar bukatar mutane su yi aiki a gonaki ya dada ta’azzara matsalar.
WPF dai ta ce barazanar na tilasta wa iyalai da dama yin kaura zuwa wasu yankunan, inda ta yi barazanar karuwar rikice-rikice in ba a kai wa mutane dauki ba.
Hukumar dai ta sha yin gargadi kan barazanar farin da kuma yiwuwar uskantar matsalar yunwa, wadanda za su iya rura wutar rikici a yankunan nahiyar da ma wasu sassa na nahiyar Asia.