Wasu da ba a san ko su wanene ba sun yi awan gaba da kayayyakin wata mota ɗauke da kayan abinci na Hukumar abinci ta duniya (WFP) a garin Gubio, yayin da take kan hanyarta ta zuwa Damasak a Jihar Borno.
Majiyar leƙen asiri ta shaidawa Zagazola Makama cewa, lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 2:30 na rana lokacin da Aminu Malam Umar direban wata babbar mota ƙirar Iɓeco ya tsaya a gefen titi.
- ’Yan adawa sun shirya ƙalubalantar Tinubu a zaɓen 2027 – Atiku
- Gobara ta ƙone gidaje tare da asarar dukiya a Gombe
Yayin da motar ta tsaya a gefen titi ba tare da kula daga jami’an tsaro ba, wasu da ba a san ko su waye ba suka sace buhunan shinkafa da gishiri da sukari da wake da kuma man girki da dama, duk da cewa ba a tantance adadin da kuma darajar kayayyakin da aka sace ba har ya zuwa yanzu.
Jami’an tsaro sun ziyarci wurin da lamarin ya faru, amma ba a kama kowa ba.
Daga bisani sojoji sun ɗauke motar zuwa Gubio lafiya lau a yayin da ake ci gaba da bincike don gano waɗanda suka aikata laifin tare da ƙwato kayayyakin da aka sace.