Wasu ’yan gida su tara sun mutu bayan cin wani abinci mai guba a kauyen Nagazi na Karamar Hukumar Adavi ta Jihar Kogi.
Aminiya ta gano cewa mutum taran sun rasu ne da maraice, bayan da rana biyar daga cikinsu sun yanke jiki sun fadi, aka kai su asibiti, kafin daga baya wasu hudu suka fadi, su ma aka kai su asibiti.
- Ana fargabar gobarar tankar mai ta kashe sama da mutum 20 a Kogi
- An binne gawarwaki 130 da aka kasa gano ’yan uwansu a Kogi
Kafin ta bayyana cewa guba mamatan su ka ci a ranar Litinin, mutanen yankin sun yi ta rade-radin cewa rasuwar wani boka ne ya yi sanadiyar mutuwar mutanen ’yan gida daya, a cewar wani mazaunin garin wanda ya bukaci a boye sunansa.
An ce bokan ya yi abubuwa na shu’umanci musu yawa da har ake tsoron sa kafin mutuwarsa kwatsam a ranar Litinin.
Su kuma, an yi zargin sun taba gawarsa ce, wanda hakan ta sa su ma suka bi shi.
Sai dai, kakakin ’yan sandan Jihar Kogi, SP Williams Aya, a hirarsu da wakilinmu, ya tabbatar masa da cewa rahoton da suka samu ya nuna, ’yan gida dayan sun rasu ne a sakamakon cin guba a cikin tuwon Amala.
Haka kuma, an samu rahoton wasu su hudu ’yan gida daya da suka mutu a lokaci guda a garinn Mopa da ke Karamar Hukumar Mopa-Muro, wadanda ake zargin amala ne ya yi ajalinsu.