A Litinin din nan wasu mutum takwas za su gurfana a gaban kuliya kan harin nan da aka kai birnin Nice na Faransa a watan Yulin 2016.
Akalla mutum 86 aka kashe a harin da wani mutum ya kai da babbar mota jim kadan bayan da dubban mutane sun kammala kallon wasan wuta a karshen bikin tunawa da ranar samun ’yan cin kai, ta Bastille Day.
Harin wanda aka tabbatar alkaluman mutum 86 da ya yi sanadiyar ajalinsu ciki har da kananan yara da samari, ya kuma jikkatar da mutum 450.
Maharin mai shekaru 31 dan Tunisiya mai suna Mohamed Lahouaiej-Bouhlel, ’yan sanda ne suka harbe shi bayan ya shafe kusan minti hudu yana mutsutstsuke mutane a gabar tekun Promenade des Anglais.
Maza bakwai da mace guda da za a gurfanar da su a gaban kuliya a birnin Paris, ana zarginsu da kulla duk wata kitimurmura da kuma ba da tallafi da gudunmawar makamai da aka kai harin da su wanda aka samu cikin motar.
Mutum daya ne kawai cikin wadanda ake zargi, Ramzi Kevin Arefa, zai fuskanci hukuncin daurin rai da rai idan aka same shi da laifi la’akari da kasancewarsa mai yawan aikata laifuka.
Kamfanin Dillancin Labarai na AFP ya ruwaito cewa, sauran na iya fuskantar zaman gidan kaso na tsawon shekaru biyar zuwa 20.
Za a soma shari’ar da misalin karfe 12:30 na rana (agogon Najeriya) kuma za ta ci gaba har zuwa tsakiyar watan Disamba lokacin da za a yanke hukunci.
Wannan dai ita ce shari’a ta baya-bayan nan da za a gudanar game da hare-haren masu tsattsauran ra’ayin addini da kuma da’awar jihadi da suka addabi Faransa tun shekara ta 2015.