Mutane takwas sun rasu, wasu 20 na kwance a asibit sakamon kuna da suka samu bayan rikicin gado ya sa wani matashi banka musu wuta a lokacin da suke sallar jam’i a cikin masallaci.
Aminiya ta kawo rahoto cewa mutanen suna cikin sallar asuba a cikin masallacin a ranar Laraba ne matashin ya shiga ya sa makamashi ya kunna wuta sannan ya kulle su ya tsere.
Shaidu sun ce kimanin mutane 40 ne ke cikin masallacin a lokacin da ya cinna wutar, lamarin da ya sa aka kai su Asibitin Kwararru na Murtala Muhammad da ke birnin Kano domin ba su kulawa.
Wakilinmu ya yi kicibus da wasu dattawa uku kowannensu na kuka cewa abokansu da dangoginsu suna nan rai-kwakwai-mutu-kwakwai a asibiti sakamakon lamarin.
- Majalisa amince wa Tinubu ciyo bashin $500m don sayen mitocin lantarki
- Manyan ’yan ta’adda sun kashe juna a Katsina
- Matashi ya cinna wa mutane wuta suna sallar Asuba a masallaci a Kano
Mazauna kauyen Larabar-Albasawa da ke Karamar Hukumar Gezawa sun bayyana cewa abin ya shafi kusan kowane gida a garin.
Kawo yanzu mutum takwas daga cikinsu sun rasu, wasu sam da 20 kuma na kwance suna karbar magani a asibiti.
Wannan lamari dai ya jefa al’ummar kauyen cikin damuwa inda suke zaman jimami da makoki sakamakon danyen da matashin mai shekaru 38 ya aikata.
Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama matashin, wanda bayyana cewa rashin gamsuwarsa da rabon gado ne ya sa ya yi wannan aika-aika a masallacin da ke gidansu a kauyen.
Aminiya ta gano cewa rikicin gado da ya ki ci ya ki cinyewa a gidansu matashin mai shekaru 38, ya bazu zuwa cikin al’ummar garin.
Shaida sun ce shi da kansa ne ya kai kansa ofishin ’yan sanda.
Wadanda aka so su yi magana kan lamarin daga cikin iyalan suna cikin wadanda abin ya ritsa da su a masallacin.
Mataimakin Shugaban ’Yan Sandan Mai Kula da Shiyya ta Daya, AIG Umar Mamman Sanda ne ya bayyana hakan yayin da shi da kwamishinan ’yan sandan jihar Kano da Daraktan Hukumar DSS da sauran shugabannin hukumomin tsaro suka ziyarci wadanda suka kone a masallacin da ke kwance a asibitin.
“Daga cikin mutane 24 da aka kawo asibiti, daya ya rasu, abin takaici ne matuka,” in ji AIG Sanda.
Ya kara da cewa, “A halin yanzu yana tare a hannunmu kuma yana bayar da bayanai masu amfani.
“Wanda ake zargin ya yi amfani da wani abin fashewa da aka kera a cikin gida domin aikata wannan mummunar ta’asa.”
“Abin da ya faru ba shi da wata alaka da ta’addanci ko wata kungiya, kawai rigima ce ta rabon gado da ta ki ci ta ki cinyewa.
“An ce wanda ake zargin bai gamsu da rabon da aka yi ba ne ya yi wannan aikin, kuma hakan a wurinsa martani ne kan abin da yake zargin an yi masa na ba daidai ba,” in ji shi.