✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutum 8 sun mutu bayan motarsu ta fada kogi a Sakkwato

Mutum takwas sun mutu bayan da motar da suke ciki ta afka cikin kogi a Karamar Hukumar Kware ta Jihar Sakkwato. Daraktan Hukumar Agajin ta…

Mutum takwas sun mutu bayan da motar da suke ciki ta afka cikin kogi a Karamar Hukumar Kware ta Jihar Sakkwato.

Daraktan Hukumar Agajin ta jihar, Mustapha Umar wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ya ce ana ci gaba da aikin gano mamatan da kuma ita motar.

“Ba mu san aihinin adadin wadanda lamarin ya rutsa da su ba, saboda ba mu samu wani ganau da yake a wajen yayin da lamarin ya auku ba.

“Sai dai gwanayen ninkayan da muka yi hayar su sun iya gano bigiren da motar take cikin kogin; inda suka shaida mana cewa karamar mota ce da za ta iya daukar mutum bakwai – ciki har da direba.

“Ko a yanzu da nake magana da kai, ana can ana ci gaba da gudanar da binciken gano gawarwakin kuma mun aika da janwe domin ciro motar daga cikin kogin”, inji shi.

Shi ma kakakin Hukumar Agaji ta Kasa, Aliyu Muhammad ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce jami’an hukumar sun dukufa domin aikin ceton.

“Har sai mun iya tantance hakikanin wadanda suke cikin motar; sa’annan ne za mu iya fadin adadin wadanda suka mutu, saboda a tashar da motar ta tashi an tabbatar mana cewa babu wata motarsu da ta gamu da wani hadari a wannan ranar – hakan na nufin ita wannan motar ba ta taso daga wannan tashar ba ke nan”, inji shi.

Aminiya ta gano cewa hatsarin ya faru ne ranar Alhamis; sai dai har kawo lokacin rubuta rahoton nan ba a kai ga gano gawarwakin mamatan da kuma motar kanta ba.

Bayanai sun ce fasinjoji bakwai ne ke cikin motar da take kan hanyar zuwa Karamar Hukumar Illela, gabanin faruwar hatsarin.

Wata majiya ta ce motar ta kade wani mutum a kan babur wanda shi ma yana daga cikin wadanda suka salwanta.