✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ƙarin ɗalibai 7 na Jami’ar Kogi sun shaƙi iskar ’yanci

Ba za mu saduda ba har sai an ceto ragowar ɗaliban da aka yi garkuwa da su.

Rundunar ‘yan sandan Jihar Kogi ta ce an kuɓutar da ƙarin wasu ɗalibai bakwai da aka sace a Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Confluence da ke yankin Osara a jihar

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, SP Williams Aya, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis.

Aminiya ta ruwaito kamar yadda hukumar ‘yan sandan ta tabbatar cewa an sace ɗalibai 24 a jami’ar kuma zuwa yanzu an ceto 21 daga ciki.

Ya ce Sufeto-Janar na ‘yan sandan Nijeriya, IGP Kayode Egbetokun, ya tura ƙwararru domin ci gaba da aikin ceto ragowar ɗaliban da ke hannun masu garkuwa da su.

“An tura sashen tsaro na rundunar ‘yan sanda na sama, wanda ya ƙunshi jami’an rundunar masu amfani da jirgi masu saukar ungulu da aka horar da su kan binciken ta sama da jami’an sa ido da kuma sashen leƙen asiri na fasaha (TIU) don ci gaba da aikin ceton da kuma kai farmaki kan masu aikata laifuka a jihar.

“Ƙwararru jami’an tsaro tare da haɗin gwiwa ne suka kai ga ceto ƙarin mutane bakwai (7) da aka sace wanda ya kawo adadin zuwa 21.

“Muna nan akan bakarmu wajen ci gaba da duk mai yiwuwa domin tabbatar da cewa an kuɓutar da dukkan ɗaliban cikin aminci tare da gurfanar da waɗanda suka aikata laifin domin a hukunta su,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa gwamnatin jihar Kogi da ma al’ummar jami’ar sun gamsu da aikin ceton da ake yi kawo yanzu.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Benthrad Onuoha, ya yaba wa Sufeta Janar ɗin bisa goyon baya kan aikin da suke gudanarwa.