✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An ceto karin daliban jami’ar Kogi 6  

Gwamnatin Kogi ta ce an sake kubutar da wasu dalibai shida daga cikin wadanda aka yi garkuwa da su daga Jami’ar kimiyya da fasaha da…

Gwamnatin Kogi ta ce an sake kubutar da wasu dalibai shida daga cikin wadanda aka yi garkuwa da su daga Jami’ar kimiyya da fasaha da ke Osara a jihar.

Kwamishinan yada labarai da sadarwa na jihar, Kinsley Fanwo ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata a Lakwaja.

Rundunar ’yan sandan jihar ta sanar da cewa an sace dalibai 24 a harin da aka kai makarantar a ranar Alhamis din da ta gabata.

A yammacin Litinin rundunar ta ce, an kubutar da dalibai 14 daga cikinsu baya musayar wuta da ’yan bindigar.

Kawo yanzu dai an tabbatar da ceto 20 saura hudu daga cikin 24 daga cikin daliban aka sace.

Kwamishinan ya ce, “An ceto dalibai tara da farko, yayin da aka samu wasu biyar da safiyar ranar Litinin, yanzu kuma an ceto wasu shida, inda adadin waɗanda aka ceto ya kai 20.

“Iyayen karin dalibai shida da aka ceto sun tabbatar da cewa daliban sun isa gida,” in ji shi.

Sanarwar ta ce gwamna Ahmed Usman Ododo ya bayyana jin dadinsa ga rundunar hadin gwiwa da ta gudanar da aikin, inda ya bukaci su cigaba da bincike har sai an ceto sauran daliban.

Gwamnatin jihar Kogi ta bai wa jama’a tabbacin cewa “an sake fasalin tsarin tsaro a yankunan makarantun jihar domin kauce wa aukuwar irin wannan a nan gaba.