Mutum biyu sun tsallake rijiya da baya da munanan raunuka bayan ayarin motocin Gwamnan, Sheriff Oborevwori sun yi mummunan hatsari.
Majiyarmu ta ce diraben daya daga cikin motocin da wani hadiman gwamnan ne suka samu rauni a hatsarin, sakamakon fashewar tayar motarsu a yayin da suke tsaka da tafiya.
Aminiya ta gano cewa an kai mutanen da abin ya shafa suna asibiti domin basu kulawa sakamakon hasarin a Asaba, fadar jihar.
Zuwa lokacin hada wannan labarin dai babu cikakken bayani game da asarar rai, amma majiyar ta ce hatsarin ya auku ne a kusa da Kwalejin Ilimi na Tarayya (Technical) da ke Asaba.
- EFCC na taimaka wa masu laifi —Oba na Benin
- Ba a Banza Matasa Ke Samun Kudi Da ‘Mining’ Ba
- Harin Masallacin Kano ya bar marayu 100, mata 13 sun shiga takaba
“Muna cikin motar haya a hanyar dawowa Asaba ne muka ji kara kamar harbi, nan da nan aka samu cunkoson ababen kafin a kai su asibiti,” in ji majiyar.
A karshe mako ne Gwamna Sheriff Oborevwori ya kai ziyara garin Warri domin halartar taron masu ruwa da tsaki na Jam’iyyar PDP ranar Lahadi gabanin zaben kanana hukumomi da ke tafe.
A hanyarsa ta komawa Asaba ne ayarin motocin nasa ya samu hatsar a safiyar Litinin.